You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837787

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

    

Source: BBC

Haaland ya ci Fulham kwallo uku rigis a Premier League

Erling Braut Haaland, Manchester City striker Erling Braut Haaland, Manchester City striker

Manchester City ta caskara Fulham 5-1 a wasan mako na huɗu a gasar Premier League ranar Asabar a filin wasanta na Etihad.

City ce ta fara cin kwallo ta hannun Julian Alvarez a minti na 31 da fara tamaula, amma minti biyu tsakani Tim Ream ya farke wa Fulham.

Daf da za su je hutu ne City ta kara na biyu ta hannun Nathan Ake a fafatawar.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Erling Haaland ya ƙara na uku, sannan ya ci na huɗu a bugun fenariti.

Haaland - wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Uefa a makon da ya gabata - ya kuma ci na biyar daf da za a tashi, kwallo uku rigis da ya ci a ranar Lahadi, sannan na shida da fara kakar bana.

Dan wasan Manchester City ya zama yana da hannu a cin kwallo 51, wanda ya ci 42 da bayar da tara aka zura a raga a wasa 39 a Premier League.

Kenan ya zama na farko da yake da hannu a zura kwallo 50 ko fiye da haka a babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan Andrew Cole da ya yi wannan bajintar amma a karawa 43.

Karo na 15 da City ta doke Fulham kenan, irin yawan nasarar da ƙungiyar Etihad ta yi kenan a kan Watforrd.

Wasa na 21 da Fulham ta yi a Etihad ba ta samu nasara ba tun bayan 3-1 da ci a Afirilun 2009.

City za ta ziyarci West Ham a wasan mako na biyar ranar 16 ga watan Satumba, yayin da Fulham za ta karbi bakuncin Luton.

Wasa na biyu a jere kenan da Pep Guradiola bai ja ragamar City ba a Premier, wanda ke jinya, amma zai halarci wasan gaba, lokacin ya gama jinya.

Read full article