BBC Hausa of Wednesday, 25 October 2023
Source: BBC
Kungiyar tsoffin daliban cibiyar koyar da dubarun mulki da tsare-tsare ta NIPS a Najeriya ta ce muddin ana son kawo karshen manyan laifukan da ke addabar Afrika sai an samu cikakken hadin kai a tsakanin kasashen nahiyar.
A wani taron da Cibiyar da ke kula da tabbatar da aikin gaskiya da jagoranci ta jagoranta a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ta bayyana girman matsalar manyan laifukan a Afrika inda ta dora laifin a kan raunin hukumomi da kuma rashin gudanar da yaki da matsalar yadda ya kamata wanda ke kara haifar da durkushewar al’amura musamman tattalin arzki da karuwar talauci da rashin aikin yi a Afrika.
Mai magana da yawun tsoffin daliban cibiyar, janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya, ya shaida wa BBC cewa, sun damu da matsalar tsaron da ke addabar nahiyar Afirka.
Ya ce, “ Idan babu hadin kai da wuya wata kasa ta ce za ta y iwa kanta maganin wadannan matsaloli, saboda yawancin laifukan kamar ta’addanci na ketara kasashe.”
Janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya, ya ce irin wadannan matsaloli na kawo nakasu ga ci gaba da walwala da kwanciyar hankali da kuma bunkasar tattalin arzikin kasashe.
Mai magana da yawun tsoffin daliban cibiyar ta NIPS, ya ce, “ Dole ya kasance an hada karfi da karfe domin a shawo kan wadannan matsaloli da suka addabi kasashen nahiyar Afirka.
Ya ce, “Mu a kungiyarmu ta tsoffin daliban wannan makaranta ta NIPS, muna kira da babbar murya ga kasashe da shugabannin kasashen Afirka a kan hada kai wajen ganin an yi maganin wadannan matsalolin tsaro da suka addabi kasashen nahiyar.”
Janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya, ya ce akwai madafan da ba sa aikin da ya dace, shi ya sa aka samu matsalolin da suka kawo tangarda ga tattalin arziki da talauci da rashin aikin yi da kuma msatalar tsaro.
Ya ce, “Da ace an inganta irin wadannan madafun, da kuma samun hadaka tsakanin kasashe da na samu saukin abubuwa.”