You are here: HomeAfricaBBC2023 04 03Article 1743113

BBC Hausa of Monday, 3 April 2023

    

Source: BBC

Hadjam bai yi wa Nates wasa ba, saboda azumin da yake yi

Mai tsaron bayan, Jaouen Hadjam Mai tsaron bayan, Jaouen Hadjam

Mai tsaron bayan, Jaouen Hadjam bai buga wa Nantes karawa da Reims ba, saboda azumin da yake yi in ji koci, Antoine Kombouare.

Ranar Lahadi Nantes ta yi rashin nasara a gida da ci 3-0 a hannun Reims a karawar mako na 29 a gasar Ligue 1.

Musulmin dan wasan da ke azumi a watan Ramadan kan samu karfin gwiwa daga kungiyar kamar yadda Kombouare ya sanar.

A kan cire dan wasa daga kalacin safe, sannan ba zai yi atisaye da yamma ba, idan ya yi da safe.

Ya kara da cewar ''Duk mai azumi ba sai ya buga gasa ba, domin bana son su ji rauni ko a samu matsala, domin sai an yi taka tsan-tsan.''

Kociyan ya kafa doka a kungiyar kuma hakan ta sa mai tsaron bayan bai buga karawar ta ranar Lahadi ba.

Kociyan ya kara da cewar ''Kawo yanzu ba wata matsala ga 'yan kwallon da ke azumi a kungiyar, a shirye nake na mara musu baya, na kwan da sani lokaci ne mai dan karen wahala a wajen 'yan kwallo.''

Nantes tana da 'yan wasa shida masu yin azumi a watan Ramadan a kakar nan, inda ake kauracewa ci da sha da wasu abubuwan laifi daga asuba zuwa faduwar rana.

Tun cikin watan Maris aka fara azumin Ramadan na shekarar nan da ake sa ran yin kusan wata daya musulmi na gudanar da shi.

Hadjam mai shekara 20 ya koma taka leda a Nantes a watan Janairu daga Paris FC.

Wasu rahotanni na cewar hukumar kwallon kafar Faransa ta hana alkalai dakatar da wasa domin 'yan wasan da ke azumi su yi buda baki ana tsaka da tamaula.

Rahoton da aka wallafa a makon jiya ya ce duk raflin da ya tsayar da wasa don a yi buda baki za a hukunta shi.

Sai dai a gasar Premier an umarci rafli su tsayar da wasa na wani dan lokaci domin bai wa 'yan wasa masu azumi su yi buda baki a gefen fili.

Read full article