BBC Hausa of Monday, 6 February 2023
Source: BBC
Sakamakon halin karancin kuɗi da al’ummar Najeriya, musamman masu ƙaramin ƙarfi suka shiga sanadiyyar sauyin fasalin wasu daga cikin manyan takardun kudin kasar na naira, masana na ganin akwai wasu hanyoyi da ya kamata hukuma da su kansu jama’a su bi domin saukaka halin da aka shiga.
A halin yanzu jama’a kan kwana ko shafe tsawon lokaci a kan layin cirar kuɗi ta na’urar banki wanda kuma duk da haka matsalar na kara ta’azzara.
A tattaunawar da BBC ta yi da Farfesa Muhammad Muttaqa, masanin tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya, yana ganin mataki na farko shi ne, ‘ ya kamata a duba ainahin matsalar a fahimci matakin da kasar take ciki tukuna kafin a ce an bullo da ire-iren wadannan tsare-tsare.‘‘
Masanin ya ce kamata ya yi a tabbatar da cewa kasa tana da wadatacciyar hanyar intanet a yawancin wurare kafin a dauki irin wannan mataki sannan kuma a tabbatar da yawaitar bankuna da kuma ilimi a tsakanin jama’a wanda duka yana ganin babu wadannan tanade-tanade, amma kwatsam gwamnati ta tunkari tsarin.
Farfesan ya ce, Najeriya kasa ce da jama’arta masu karancin ilimi suke da yawa, ilimi na yau da kullum da kuma ilimin sanin hada-hadar banki wanda kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da wannan kana ta yi dabarun da za su rage nakasun da za a iya samu daga irin wannan rukuni na al’umma da ke baya a harkar ilimi kafin a samu nasarar karbuwar tsarin.
Sannan ya ce uwa-uba‚ ‘duka wannan tsari na hada-hadar kudi ta waya da intanet abu ne da ya ta’allaka da yarda da amana a tsakanin jama’a, wanda kuma akwai karancin wannan a tsakanin mutane saboda haka abu ne da yake da wuya ya yi nasara, har sai an samu wannan yarda da amana.
Masanin yana ganin tun da farko ya kamata a ce hukuma ta tashi tsaye haikan ta fadakar da jama’a amfanin da ke tattare da duka irin wadannan tsare-tsare nata kafin ta bullo da su ta yadda jama’a za su lamunta da su da zarar ta zo aiwatar da su.
Farfesan yana kuma ganin akwai bukatar gwamnati ta samar da yanayi na nuna wa matasa masu ilimi da fasahar intanet da sauran jama’a kishin kasa ta yadda za su rika amfanar da kasar da baiwar da suke da ita a wannan fanni maimakon amfani da ilimin ta hanyar zamba.
Mece ce mafita?
Dakta Muhammad Shamsuddin na Jami‘ar Bayero da ke Kano, yana ganin halin da al’ummar Najeriyar ke ciki a yanzu dangane da matsalar karancin kudin mafitarta yawanci na hannun gwamnati.
Ya ce ya kamata Babban Bankin kasar ya samar da karin kudi ta yadda jama’a za su wadata daidai gwargwado da abin da suke bukata, yana mai cewa ‚‘ a halin da ake ciki mutane su kansu sun kara ta’azzara matsalar ta yadda suke boye kudi kamar gwal ba sa son saki ta yadda zai kewaya a tsakanin al’umma.‘‘
Ya ce, 'yan siyasa suna boye kudi saboda harkar zabe, yayin da manyan jami’an bankuna suma suke boye kudin domin bayar da su ga manyan masu hali, haka daidaikun mutane suma idan sabbin kudin sun shiga hannunsu ba sa son saki.
Abubuwan da mutane za su iya yi
Daina ɓoye kuɗi:
Masana kamar Dakata Shamsudden Muhammad na ganin ya kamata mutane su dina ɓoye kuɗi saboda tsoron rashin wadatuwarsu.
A cewar shi hakan na ƙara ta'azzara matsalar, saboda haka nan ya kamata mutane su ci gaba da hada-hada da kuɗaɗen da suke da su a hannunsu.
Haka nan sun yi kira ga ƴan siyasa da su daina ɓoye kuɗaɗe domin kashewa a lokacin zaɓe.
Masanin ya ce to wannan na daga cikin manyan abubuwan da ke kara jefa jama’a cikin halin da ake ciki na karancin kudin, ‘dole sai kudi na musayar hannu tsakanin jama’a kafin al’amura su yi sauki, mutane su san cewa ba wai an yi kudi ba ne domin su rike su su ki saki.‘‘
Kiraye-kiraye ga gwamati:
Masanin tattalin arziƙi Shu'abi Idris Mikati ya ce ya kamata mutane su ci gaba da kiraye-kiraye ga gwamnati domin ganin ta ɗauki matakan da za su kawo sauƙi.
A cewar sa "yawan kiraye-kirayen zai iya tursasa wa gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace."
Ya ƙara da cewa wannan yanayi ya haifar da mummunar matsala ga al'umma.
Cinikin ba ni gishiri in ba ka manda:
Duk da ba abu ne da yake da sauki a yanzu ba, wasu daga cikin masanan na ganin cewar cinikayyar ba ni gishiri in ba ka manda zai iya taimakawa a wasu yankuna, musamman na karkara.
Sai dai a cewar Shua'aibu Mikati, "kamar ni da nake a Legas yanzu, mene ne nake da shi da zan bai wa mai sayar da lemu a baro domin ya ba ni lemun, in dai ba aiki zan yi masa?"
eNaira:
eNaira tsari ne da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙirƙiro domin sauƙaƙa harkar kasuwanci.
Masanin harkokin kuɗi Aminu Aminu Bizi ya ce eNaira manhaja ce da mutane za su iya saukewa a wayoyinsu su rinƙa amfani da ita wurin aikawa da kuma karɓar saƙonnin kuɗi.
Ya ce masu ƙananan sana'o'i kamar na fiyawata, da masu ƙosai ko sayar da kifi za su iya amfani da tsarin.
Ya ƙara da cewa duk da tsarin yana amfani ne da 'netwok' na wayar salula, amma za a iya amfani da shi har a wuraren da babu netwok ɗin, inda da zarar aka je inda ake da netwok kuɗaden da aka tura za su shiga.
Bayan sauya fasalin takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000 Babban Bankin Najeriya ya sanya wa’adin zuwa ranar 31 ga watan Janairu da ya kare domin daina karbar tsoffin kudin.
Amma kuma bayan matsin lamba saboda halin da jama’a suka shiga na wahala, sai bankin ya kara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu 2023, tare da cewa bankin zai ci gaba da karbar tsoffin kudin yana sauya wa jama’a da sababbi ko da wa’adin ya kare amma kuma su jama’a a tsakaninsu ba za su ci gaba da amfani da tsoffin ba bayan wa’adin.
Duk da wannan mataki na Babban Bankin na Najeriya har yanzu ana nuna rashin gamsuwa da tsarin sauyin kudin da kuma manufar bullo da tsarin takaita amfani da kudi a hannu tsakanin jama’a saboda ana ganin kasar ba ta samar da muhimman abubuwan da za su tabbatar da nasara da karbuwar shirin ba.