You are here: HomeAfricaBBC2023 02 05Article 1708628

BBC Hausa of Sunday, 5 February 2023

    

Source: BBC

Har yanzu Liverpool ba ta ci wasan Premier ba tun shiga 2023

Jurgen Klopp, kocin Liverpool Jurgen Klopp, kocin Liverpool

Liverpool ta yi rashin nasara da ci 3-0 a hannun Wolverhampton a wasan mako na 22 a gasar Premier League ranar Asabar.

Da wannan sakamakon Liverpool , wadda ta yi wasa 20 tana ta 10 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 29.

Wasa na bakwai kenan da Liverpool ta kara a shekara 2023, kuma daya daga ciki yi nasara shi ne a FA Cup da ta doke Wolves 1-0.

To sai dai har yanzu Liverpool ba ta karawa ba a gasar Premier a 2023 a wasa hudun da ta fafata kawo yanzu.

Cikin wasannin da kungiyar Anfield ta buga a bana har da wanda Brighton ta fitar da ita a FA Cup, duk da cewar ita ce ke rike da kofin.

Liverpool ta yi ta biyu a bara a kakar da Manchester City ta duki Premier League a ranar karshe.

Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ce ta lashe Carabao da FA Cup a babar da buga wasan karsahe a Champions League da Real Madrid ta dauka a Faransa.

Ranar Litinin Liverpool za ta kara da Everton a gasar Premier League a Anfield daga nan ta ziyarci Newcastle ranar Asabar a dai babbar gasar tamaula ta Ingila.

Daga nan kuma Liverpool za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan farko na kungiyoyi 16 a Champions League da za su fafata ranar 21 ga watan Fabrairu.

Jerin wasannin da Liverpool ta buga a 2023:

Premier League Litinin 2 ga watan Janairu



  • Brentford 3 - 1 Liverpool

FA CUP Asabar 7 ga watan Janairu



  • Liverpool 2 - 2 Wolves

Premier League Sa 14Jan 2023



  • Brighton 3 - 0 Liverpool

FA CUP Talata 17 ga watan Janairu



  • Wolves 0 - 1 Liverpool

Premier League Asabar 21 ga watan Janairu



  • Liverpool 0 - 0 Chelsea

FA CUP Lahadi 29 ga watan Janairu



  • Brighton 2 - 1 Liverpool

Premier League Asabar 4 ga watan Janairu



  • Wolves 3 - 0 Liverpool

Wasa uku na gaba da Liverpool za ta buga

Premier League Litinin 13 ga watan Fabrairu



  • Liverpool da Everton

Premier League Asabar 18 ga watan Fabrairu



  • Newcastle da Liverpool

Champions League Talata 21 ga watan Fabrairu



  • Liverpool da Real Madrid







Read full article