You are here: HomeAfricaBBC2021 08 25Article 1341364

BBC Hausa of Wednesday, 25 August 2021

    

Source: BBC

Harry Kane: Dan kwallon Tottenham ya ce zai ci gaba da zama a kungiyar

Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila

Kyaftin din tawagar Ingila, Harry Kane ya ce zai ci gaba da zama a Tottenham a kakar bana, zai mayar da hankali kan samarwa da kungiyar nasarori.

Tun farko an sa ran Manchester City ce za ta dauki dan kwallon a kakar nan, bayan da ya nemi izinin barin kungiyar daga shugaba Daniel Levy.

Sai dai Levy bai yadda ya kulla wata sabuwar yarjejeniya da dan wasan mai shekara 28 ba.

Kane ya buga wa kungiyar wasan farko a bana a Premier League da Tottenham ta je ta doke Wolverhampton 1-0 a Molineux.

Kocin kungiyar, Nuno Espirito Santos ya ce labari mai kyau ne da Kane ya kawo karshen makomar sa a Tottenham da cewar zai ci gaba da zama.

Tottenham za ta fuskanci Pacos de Ferreira a Europa Conference League ranar Alhamis, bayan da ta yi nasara a wasan farko da ci 1-0 a fafatawar cike gurbi.

Kane wanda kwantiragin sa zai kare a karshen kakar 2024, ya sanar zai ci gaba da taka leda a Tottenham, saura kwana shida a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai ranar 31 ga watan Agusta.

Kyaftin din tawagar Ingila bai buga wa Tottenham wasan makon farko da Tottenham ta ci Manchester City 1-0 a gasar Premier League da karawa da Pacos de Ferreira a Europa Conference League.

Read full article