You are here: HomeAfricaBBC2021 08 10Article 1329664

BBC Hausa of Tuesday, 10 August 2021

    

Source: BBC

Isa Abba Adamu: Ana alhinin rasuwar tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC

Tsohon shugaban sashen Hausa na BBC, marigayi Malam Isa Abba Adamu Tsohon shugaban sashen Hausa na BBC, marigayi Malam Isa Abba Adamu

'Yan uwa da abokan aiki na ci gaba da bayyana jimaminsu na rasuwar tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC, Malam Isa Abba Adamu.

Ya rasu ne a birnin London a karshen mako bayan gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 60 a duniya.

Fitaccen dan jaridar, wanda ya kwashe fiye da shekaru 20 yana aiki da BBC, ya bar mata daya da 'ya'ya hudu.

Ya soma aiki a BBC Hausa matsayin mai shirya shiri inda ya rika samun ci gaba.

Shi ne bakar fata na farko da ya zama shugaban Sashen Hausa na BBC mai cikakken iko.

Kazalika, Malam Isa, ya rike mukamin shugaban Sashen Afirka na BBC.

An haifi marigayin a shekarar 1961 a birnin Kano da ke arewacin Najeriya, kuma ya kammala digirinsa na farko a Jami'ar Bayero a shekarar 1985.

Kafin ya soma aiki da BBC Hausa, ya yi aiki a Kano State Television CTV 67.

'Aiki tuƙuru'

Malam Sulaiman Ibrahim, wani tsohon ma'aikacin BBC Hausa wanda kuma ya taba yin aiki tare da marigayi Isa Abba Adamu, ya bayyana shi a matsayin mutum mai jajircewa wurin aiki.

"Isa Abba Adamu mutum ne ma'aikaci. Yana aiki tukuru; idan yana aiki ba ka ganin ya tsaya yana wasa. Idan labarai yake yi ko kuma shirya gabatarwa, idan ka ga [Isa] ya tsaya yana lamari, to ya kammala abin da zai shiga ya karanta ke nan," a cewarsa.

Ya kara da cewa abin da za a fi tunawa game da marigayi Isa Abba Adamu shi ne "yadda duk sadda ya zo tsakiyar shiri, idan ya ce 'ana sauraren Sashen Hausa na BBC ne, to sai ya ce daga tsakiyar birnin London ni kuma ni ne Isa Abba Adamu."

Read full article