BBC Hausa of Monday, 21 August 2023
Source: BBC
Likitoci da yawa sun shawarci Farah Nurfirman ta bar garinta Jakarta ta koma wani garin domin lafiyarta.
Matashiyar mai shekara 22 tana fama da larurar numfashi ta asma, abin da ya sa ko da yaushe take sa safar fuska (takunkumi), ta rufe hanci da bakinta.
Sannan kuma ba ta rabuwa da abar shakawar nan ta masu cutar, amma duk da haka ba ta tsira ba saboda gurɓatacciyar iskar garin.
Babban birnin na Indonesia, wanda ya daɗe yana fama da matsalar gurɓatar iska, ya kasance birnin da ya fi fama da gurɓatacciyar iska a faɗin duniya kusan a kullum, cikin makon da ya gabata a alƙaluman da ake fitarwa.
Saboda tsananin matsalar ne ma a ranar Litinin Shugaba Joko Widodo ya bayar da umarni cewa ma’aikatan gwamnati su rika aiki daga gida.
A makon da ya gabata gubar da take gurɓata iskar ta Jakarta (PM2.5 ) ta ƙaru sosai har ma ta fi ta sauran biranen da ke da irin wannan matsala a duniya, kamar Riyadh, da Doha da kuma Lahore, kamar yadda alƙaluman da wani kamfanin Switzerland da ke fitar da bayanai a kan gurɓatar iska IQAir ya fitar.
Kamfanin yana fitar da alƙaluman gurɓatar iska a dukkanin manyan biranen duniya kullum, kuma kai tsaye.
Tun a watan Mayu ake shigar da birnin na Jakarta cikin jerin birane 10 na duniya da suka fi samun matsalar guɓatar iska.
Babban birnin da sauran garuruwa da ke kewaye da shi suna da mutum kusan miliyan 30 da ke zaune a cikinsu.
A kwanan nan Farah, har wata na’ura take yawo da ita, wadda take nuna wa mutum yawan iskar da ke cikin jininsa, (oximeter), domin ya kauce wa shiga haɗarin matsalar ta asma saboda rashin wadatacciyar iska a jininsa.
Farah, wadda take aiki a matsayin mai neman sanin makama a wani kamfanin tallace-tallace, ta ce, “mutanen da suke da cutar asma, ko da kaɗan yawan iskar cikin jininka ta ragu, za ka iya ji sosai, ba wai kawai ɗaɗɗaurewar jiki ba ne kaɗai, hatta ƙirjina ma ciwo yake sosai. Mutum na fama sosai wajen numfashi.”
"Asmata tana da tsanani kuma gadonta na yi. Kowa ne likita ce min yake na bar Jakarta kawai. 'Ki bar Jakarta idan kina son ki samu lafiya, idan ba haka ba za ki ci gaba da zama a wannan hali, abin da suke gaya min ke nan."
"Na gaji sosai saboda ba abin da zan iya yi. Saboda ni a nan nake zaune. In bayan sanya takunkumi, ba wani abu kuma da zan iya yi," in ji Farah.
Hukumomin ƙasar na ɗora alhakin ƙaruwar gurɓatar iskar a kan shigowar lokacin rani da kuma hayaƙin motoci da sauran ababan hawa, kuma sun ce nan da wani lokaci za su ɗauki matakin binciken ababen hawa domin tilasta musu zuwa gwajin yawan hayaƙin da suke fitarwa.
Shugaba Widodo ya nemi a riƙa amfani da fasahar nan ta yin ruwan sama a yankin babban birnin na Jakarta, sannan ya shawarci kamfanoni su ɓullo da tsarin yin aiki daga gida a wani lokacin.
Haka ita ma hukumar birnin tana duba yuwuwar ɓullo da tsarin da rabin ma’aikatanta za su riƙa aiki daga gida.
To amma kuma mazauna birnin na Jakarta kamar su Juan Emmanuel Dharmadjaya sun samu kansu a hali na tsaka-mai-wuya.
Ya ce, "gaskiya ni ina son zama a Indonesia saboda a nan aka haife ni kuma a nan iyalina suke da zama. To amma gurɓatacciyar iskar na yi wa mutane kisan mummuke."
Mutumin mai shekara 22 ya taɓa kamuwa da cutar tarin fuka, yanzu kuma yana fama da matsalar toshewar hanci.
Ya ce, matsalar ta gurɓatacciyar iska na yin illa ga lafiyarsa.
"Ba zan iya mayar da hankalina sosai a kan rayuwata ta yau da kullum ba, saboda kusan kullum ina fama da yoyon hanci da kuma ƙaiƙayi," in ji Juan, wanda ke aikin kwamfuta.
Da ya kwatanta da lokacin da yake zaune a Jamus yana karatu, ya ce: "A Turai, ban taɓa samun kaina a wannan yanayin da hancina ke yoyo ko tari ba, ko da kuwa a lokacin tsananin sanyi ne. To amma lokacin da na dawo Jakarta, nan da nan sai hancina ya bushe. Abin ba kyawun gani kuma yana toshewa."
Wani babban jami’i a Ma’aikatar Muhalli da Dazuka ta Indonesia, Sigit Reliantoro, a ranar Juma’ar da ta gabata ya gaya wa manema labarai a yayin wani taro cewa busasshiyar iska da ake samu a watan Yuni da Yuli da kuma Agusta, ta haddasa ƙaruwar gurɓatar yanayin a Jakarta.
Busasshiyar iska daman tana sa abubuwan da ke gurɓata iska su kasance a cikin iska tsawon lokaci.
Haka kuma a irin wannan lokaci aka fi samun gobarar daji, domin yanayi ne na rani.
Sigit, ya ce binciken da gwamnati ta yi ya nuna cewa hayaƙin da motoci ke fitarwa shi ke haddasa kashi 44 cikin ɗari na gurɓatacciyar iska.
To amma masu fafutukar yaƙi da gurɓata yanayi, irin su Muhammad Aminullah suna ganin masana’antu da kuma manyan injina da ake amfani da kwal wajen samar da makamashin tafiyar da su, su ne ainahin abubuwan da ke gurata iskar Jakarta.
Duk da cewa Indonesia tana da babban burin rage yawan hayaƙin da ke gurɓata yanayi, misali ta hanyar daina amfani da kwal nan da shekara ta 2056, a yanzu ita ce ƙasar da ta fi kowacce a duniya fitar da kwal zuwa ƙasashe.
Daina amfani da kwal din shi kansa yana da wata matsalar ta daban, saboda yawan mutanen da ke aiki a masana’antun da ke da alaka da kwal ɗin.
Gwamnati ba ta iya ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran mataki ba a kan waɗannan masana’antu saboda, ra’ayi na tattalin arziki da kuma siyasa, in ji Aminullah, wanda kuma ke jagorantar wani dandali na inganta muhalli, da ake kira Walhi.
Ya ce, ba a zubar da tokar da kwal ɗin ke fitarwa yadda ya kamata, ko da kuwa wannan masana’anta a kusa da garin da jama’a suke aka yi ta.
Amrin (ba sunansa na gaskiya ba ke nan), wanda yake zaune a kusa da wata masana’anta da ake amfani da kwal na daga cikin waɗanda matsalar ta shafa.
Ya gaya wa BBC cewa shi da iyalinsa suna adana ruwan sama domin sha da wanka. To amma tun da wannan masana’anta ta fara aiki a 2009, ba sa samun ruwa mai kyau.
Ya ce,"ba ma ko gwada yin hakan yanzu saboda za ka ruwan ya yi baki, ga kuma kauri da ya yi da ƙura baƙa."