BBC Hausa of Tuesday, 2 May 2023
Source: BBC
Ƴan majalisa a Japan na ƙoƙarin bijiro da wasu dokoki a karon faro don yaƙi da ɗabi'ar ɗaukar hoto ko bidiyon tsiraici don ci da gumin wasu, ba tare da izininsu ba.
Ƙudurin dokar zai haramta ɗaukan hoto ko naɗar bidiyon tsiraicin mutum a asirce.
Ana gurfanar da irin waɗannan laifuka a ƙarƙashin dokokin yanki da suka bambanta sosai a ƙasar.
Ƙudurin wani ɓangare ne na garambawul kan dokokin Japan game da laifukan da suka shafi cin zarafin lalata wanda kuma zai faɗaɗa ma'anar fyaɗe.
Ƙudurin ya haramta ɗauka ko yaɗawa ko ma ajiye hotunan al'aurar wasu, ba tare da izininsu ba.
Ya kuma haramta ɗabi'ar ɗaukan hotunan mutanen da ake yaudara, a kuma ɗauki wani ɓangare na al'aurarsu ba tare da saninsu ba.
Taƙamaimai ƙudurin ya hana ɗaukar bidiyon al'aurar ƙananan yara ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
A Japan, ana yi wa yara masu tallata kayan ƙawa - akasari mata - wani bahagon kallo. Misali, wasu ana neman su sanya tufafi irin na masu ninƙaya ko ɗan kamfai.
A cewar rahotanni daga kafafen yaɗa labaran ƙasar, wani lokacin ana amfani da hotunan ƴan wasa sanye da kayan tsere domin wata manufa ta lalata ko kuma wata nifaƙa.
Waɗanda aka samu da laifi, za su fuskanci ɗaurin kusan shekara uku a gidan yari ko kuma tarar kusan yen miliyan uku na kuɗin Japan - kwatankwacin dala dubu ashirin da biyu.
Ana sa ran za a amince da gyare-gyaren a cikin watan Yunin bana.
Lamarin na zuwa ne sakamakon ƙorafin da jama'a suka yi na neman tsaurara dokoki don haramta laifukan ɗaukar hoto ta wayoyin hannu.
A 2021 ne, ƴan sandan Japan suka kama sama da mutum 5,000 saboda ɗaukar hotunan mutane cikin sirri - abin da ya ninka har sau uku na yawan mutanen da aka samu a 2010.
Kusan ma'aikatan jirgin sama bakwai cikin 10 a Japan sun ba da rahoton cewa an ɗauke su hoto a asirce, a cewar wani bincike da ƙungiyar ma'aikatan sufurin jiragen sama ta ƙasar ta wallafa a watan Maris.
Da ma tuni, akasarin masu ƙera wayoyin hannu a Japan suka sanya wani sauti na ƙararrawa a wayoyin salula domin hana naɗar bidiyo cikin sirri.
Ƙasashen Asiya da dama suna da dokokin da ke yaƙar irin wannan cin zarafi, sai dai aiwatar da dokokin ya bambanta.
A Koriya ta Kudu, waɗanda aka samu da laifin naɗar bidiyo ko ɗaukar hoton lalata a asirce na fuskantar tarar kusan won miliyan 10, kimanin dala 7,500 ko kuma ɗaurin shekara bakwai a gidan yari.
Sai dai ƙungiyar lauyoyi mata a Koriya ta ce kashi biyar cikin 100 na ƙararraki 2,000 da suka shafi ɗaukar hotuna ba bisa ƙa'ida ba da aka kai gaban kotu tsakanin 2011 da 2016, sun kai ga ɗauri.
A Singapore, wanda aka samu da laifin kallon bidiyo ko hotunan tsiraicin mutane na iya fuskantar ɗaurin shekara biyu a gidan yari, ko tara ko kuma bulala ko ma haɗakar waɗannan hukunce-hukunce.
Satar ɗaukar hotunan lalata da aka aikata da yaran da shekarunsu ba su wuce 14 ba, na nufin ɗaurin dole a gidan yari, haɗi da tara da kuma bulala.
Japan na duba sauye-sauye a dokokin hukunta laifuka da dama domin ƙarfafa dokar yaƙi da laifukan da suka shafi jima'i, bayan da jama'a suka yi ta ƙorafi saboda wanke mutane da dama daga zargin fyaɗe a 2019.
A watan Fabrairun bana, wani kwamitin ma'aikatar shari'a a Japan ya bayar da shawarar ƙara shekarun da mutum zai iya kai wa kafin a shari'ance ya isa yarje wa abokin jima'i daga 13 zuwa 16.
Sannan za a ƙara tsawon shekarun da za a iya shigar da ƙarar aikata fyaɗe daga shekara 10 har zuwa sha biyar.
A yanzu haka, Japan tana da mafi ƙarancin shekarun cikar balaga na mutumin da zai iya yarda a shari'ance a yi jima'i da shi a tsakanin ƙasashen da suka ci gaban tattalin arziƙi.