You are here: HomeAfricaBBC2021 07 01Article 1299538

BBC Hausa of Thursday, 1 July 2021

    

Source: BBC

Juventus ta tafka hasara za ta sayar da hannun jari

Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus

Kungiyar Juventus ta ce ta tafka hasarar fam miliyan 275, sakamakon cutar korona.

Juventus ta ce za ta sayar da hannun jari don hada kudi fam milyan 343.25, don rage radadin tattalin arziki da cutar ta jefa ta.

Kungiyar ba ta lashe Serie A ba a kakar bana, kuma a karon farko tun bayan 2012, ta dai samu gurbin shiga Champions League a kakar 2021/2.

Kawo yanzu Juventus na fuskantar fushin Uefa, saboda kin janyewa daga shirin kafa gasar European Super League da tsarin bai samu karbuwa ba tare da Real Madrid da Barcelona.

Wasu na bin bahasin yadda ake gudanar da kasuwanci a kungiyar, tun bayan da ta dauki Cristiano Ronaldo kan fam miliyan 99.2 daga Real Madrid a shekarar 2018.

An dauko Ronaldo ne don kungiyar ta lashe Champions League, amma tun zuwansa Italiya Juventus ba ta taba haura quarter finals ba, an kuma fitar da ita a gasar a karawar zagaye na biyu a kaka biyu da ta wuce.

Kungiyar ta sanar cewar Maurizio Arrivabene, zai karbi aikin kasuwancin Juventus,

Hakan na nufin Arrivabene wanda ya yi aiki da kamfanin Ferrari a Formula 1 zai maye Gurbin Fabio Paratici, wanda ya bar kungiyar zuwa Tottenham a watan Mayu a matsayin daraktan wasannin kungiyar.

Read full article