You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809575

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

    

Source: BBC

Kane baya son komawa PSG, West Ham na son Maguire

Harry Kane Harry Kane

Ɗan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, ba ya son koma wa kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain a kakar bana, ɗan wasan mai shekara 29 da ake ganin ya fi karkata zuwa Bayern Munich zai yi watsi da duk wani tayi da gwarzuwar Faransan ta yi masa. (Telegraph - subscription required)

Idan Kane ya bar ƙungiyar, da yiwuwar Tottenham ɗin nemi ɗaukar ɗan wasan gaban Brentford Ivan Toney mai shekara 27 wanda yanzu haka aka dakatar da shi daga taka leda har zuwa Janairun 2024. (Football Transfers)

A karon farko tun bayan da ya aike da wasikar rashin tsawaita kwantigiransa ga kungiyar PSG, dan wasan gaban Faransa Kylian Mbabbe zai hadu gaba da gaba da shugaban kungiyar PSG, Nasser Al-Khelaifi. (Sky Sports)

A wannan makon ana sa ran Chelsea za ta ƙara taya ɗan wasan tsakiyar Brighton Moises Caicedo kan farashin fiye da fam miliyan 70 wanda shi kuma tuni ya amince da sharudan kungiyar. (Standard)

Shi kuwa dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, ya shirya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar Manchester United, kwantiragin da za ta kai har zuwa 2028, kuma zai riƙa karɓar fam 325,000 a duk mako. (Times - subscription required)

West Ham ta taya dan wasan tsakiyar Portugal Joao Palhinha mai shekara 28 kan fam miliyan 45, wanda kuma Fulham da ki amincewa da tayin, yayin da Manchester United kuma ta samu kwankwasa kofa daga Hammers na daukar dan wasan bayanta Harry Maguire mai shekara 30. (Guardian)

Ita kuwa West Ham ta bi sahun Manchester United na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Bayern Munich kuma dan tsakiyar Jamus Leon Goretzka. (Sky Germany)

Ana kyautata zaton Inter Milan za ta taya dan wasan gaban Amurka Folarin Balogun a kan fam miliyan 34, wanda Arsenal ta fara yunkurin dauka kan kudi kan fam miliyan 50. (Athletic - subscription required)

Brighton na kan gaba a rige rigen daukar matashin dan wasan Ingila Cole Palmer aro daga Manchester City, yayin da Burnley da Leicester City suma ke zawarcinsa. (Telegraph - subscription required)

Kazalika Brighton din na shirin shan kan Fulham wajen daukar ɗan bayan Brazil Igor. (Standard)

Su kuwa Burnley da Leicester da kuma Sheffield United, na kan kulla yarjejeniyar aron dan wasan Manchester United Amad Diallo. (Mail)

Wolverhampton Wanderers na tattaunawa a kan daukar dan wasan bayan Switzerland Nico Elvedi mai shekara 26 daga Borussia Monchengladbach. . (Express & Star)

Leeds United ta amince da yarjejeniyar daukar dan wasan bayan Wales Ethan Ampadu kan fam miliyan bakwai. . (Athletic - subscription required)

Read full article