BBC Hausa of Monday, 14 August 2023
Source: BBC
Tattalin arzikin China na ci gaba da samun tasgaro, a yayin da farashin kayayyaki suka faɗi ƙasa warwas a watan Yuli - karon farko cikin fiye da shekara biyu.
Farashin kayayyaki - wanda ake amfani da su wajen auna hauhawar farashi - ya faɗi da kaso a ƙalla 0.3 a watan da ya gabata.
Masu sharhi sun ce hakan ya ƙara matsin lamba kan gwamnati don sake farfaɗo da yawan buƙatar kayyayaki a ƙasar, wadda ita ce ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Hakan na zuwa ne sakamakon raunin da aka fuskar a ɓangaren shiga da fitar da kayayyaki a ƙasar, wanda ya aza ayar tambaya game da matakan da ƙasar ke ɗauka domin farfaɗo da tattakin arzikin ƙasar tun bayan gushewar annobar Korona.
Haka kuma China na fama da matsalar bayar da ƙananan basuka ga 'yan kasuwa, ga kuma kalubalen samun hayar shaguna.
Sannan batun rashin aikin yi tsakanin matasa, wanda a wannan shekara ya kai matsayin da bai taɓa kai wa ba.
A bana matasa miliyan 11.58 ne za su kammala jami'a a China, sannan kuma su faɗa fafutikar neman aiki.
Faɗuwar farashin kayayyaki ta tsaurara wa ƙasar rage basukan da ake binta, kamar yadda masu sharhi ke cewa.
Yaushe farashi ya fara karyewa a china?
Ƙasashen duniya da dama sun samu bunƙasa a harkokin kasuwancinsu bayan shuɗewar matakan taiƙaita zirga-zirga a lokacin annobar Korona.
Mutanen da suka taskance kuɗaɗensu sun fito da kuɗin cike da muradin yin sayayya, inda 'yan kasuwa suka riƙa ƙoƙarin yadda za su gano abubuwan da aka fi buƙata domin sarowa.
To amma hakan bai kasance a China ba, inda farashin kayyakin ya ƙi tashi tun bayan janye dokokin annobar korona, farashin kayayyaki ya karye tun watan Fabrairun 2021.
Hasali ma ƙasar ta kwashe watanni tana fama da karyewar tatalin arziki, wanda ya ƙara ta'azzara a wannan shekara sakamakon raguwar buƙatun kayyakin.
Farashin kayayyakin da ake sarrafawa a kamfanoni na ci gaba da faɗuwa a China.
Farfesa Alicia Garcia-Herrero ta jami'ar kimiyya da fasaha ta Hong Kong ta ce ''lamarin abin tayar da hankali ne, yadda ake samun raguwar buƙatar kayayyaki a China, yayin da ake samun ƙaruwar buƙatar a wasu ƙasashe, musamman ƙasashen yamma''.
''Karyewar farashi ba zai amfani China ba. basuka za su ƙara yi mata nauyi. wannan ba a bu ne mai daɗi ba'', in ji ta.
Me ya sa karyewar farashi ke zama matsala?
Ƙasar China ce ke sarrafa kaso mai yawa na kayyakin da ake sayarwa a duniya.
Karyewar farashin kayayyaki a ƙasar ya sa farashin ya tashi a wasu ƙasashen duniya, ciki har da Birtaniya.
Idan karyewar farashin kayyakin China ta yi tasiri kan kayyakin da take fitarwa zuwa ƙasashen duniya, hakan zai haddasa faɗuwar farashin kayayyakinta a ƙasashen waje, lamarin da zai shafi kasuwanci da zuba jari a ƙasar.
Faɗuwar farashin, za ta kuma shafi riba da kuɗaɗen da kamfanoni ke samu, lamarin da zai iya haddasa ƙaruwar rashin aikin yi a ƙasar, sakamakon rage ma'aikata da kamfanonin za su yi.
Haka kuma abin zai haddasa raguwar buƙatar kayayaki a ƙasar - wadda ta fi kowace ƙasa harkokin kasuwanci a duniya - kamar su makamashi, da abubuwan da kamfanoni ke buƙata da abinci, wanda zai shafi fitar da abinci zuwa ƙasashen waje.