BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023
Source: BBC
A Najeriya kashin farko na daliban kasar daga Sudan waɗanda ke guje wa yaki sun isa gida da talatainin dare, ranar Laraba.
Daliban wadanda suka sauka da misalin ƙarfe 11:30 na dare a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja na daga cikin kason farko da suka samu ficewa daga Sudan ta kasar Masar.
Tun farko a yammacin Larabar ne hukumomin Najeriyar suka bayyana cewa jirgin na farko ya taso daga filin jirgin sama na birnin Aswan da ke Masar.
Hakan dai na zuwa ne sama da mako biyu bayan barkewar fada a Khartoum, babban birnin Sudan.
Sudan ta fada cikin wani yanayi ne bayan fito-na-fito tsakanin bangarori biyu na mayaka a kasar.
Alkaluma daga hukuma sun bayyana cewa rayukan daruruwan mutane sun salwanta ya zuwa yanzu, sai dai babu sahihin bayani kan yawan wadanda suka mutun.
Kasashe da dama sun gaggauta wajen ganin sun kwashe ‘yan kasarsu, sai dai Najeriya ta fuskanci tsaiko bayan kalubale da dama.
A ranar Laraba ne Birtaniya ta sanar da kammala kwashe ‘yan kasarta, a daidai lokacin da jirgi na farko da zai kwaso ‘yan Najeriya mazauna Sudan din ke shirin baro Masar.
Yanzu haka dai akwai sauran dubban ‘yan Najeriyar mazauna Sudan da suke jiran a kwaso su, wadanda galibi dalibai ne da ke karatu a jami’o’i daban-daban na kasar.
Bay aga daliban da ake sa ran za su baro Sudan din ta kasar Masar, akwai wasu daliban da suke birnin Port Sudan, wadanda ake sa ran za su tsallaka Saudiyya ta bahar Maliya kafin jirgi ya kwashe su daga Jiddah zuwa gida Najeriya.