You are here: HomeAfricaBBC2021 08 20Article 1337248

BBC Hausa of Friday, 20 August 2021

    

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Lingard, Lewandowski, Salah, Mbappe, Aubameyang da Saar

Jesse Lingard, dan wasan tsakiyar Manchester United da Ingila Jesse Lingard, dan wasan tsakiyar Manchester United da Ingila

Dan wasan tsakiyar Manchester United da Ingila Jesse Lingard ya ce a shirye yake ya bar kungiyar kafin a rufe kasuwar cinikin yan wasa.

Lingard, mai shekaru 28 wanda ya haska sosai a kakar bara da West Ham a matsayin aro, ya ce matsawar Ole Gunner Soskjaer ba zai ba shi tabbacin zai rika sanya shi wasa akai-akai ba, to ya ba shi dama ya tafi. (Times - subscription required)

Liverpool ta shirin baiwa dan wasan gaban Egypt Mohamed Salah sabuwar kwantiragi kamar yadda jaridar Athletic ta rubuto. (Athletic - subscription required)

Ita kuma Sheffied United ta nuna sha'awar karbar dan wasan Manchester United Amad Dialo mai shekaru 19 a matsayin aro. (Sky Sports)

Jaridar Mirror ta ruwaito cewa dan wasan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski na son barin kungiyar. (Mirror)

Anan kuma kungiyoyin Chelsea da Manchester United na ja-in-ja kan Aurelien Tchouameni na Monaco. (Simon Phillips, via Express)

Pierre-Emerick Aubameyang ya ce yana sha'awar ci gaba da zama a Arsenal duk da Barcelona ta nuna sha'awar dauko dan gaban Gabon din mai shekaru 32. (Express)

Shi kuwa mai horar da PSG Mauricio Pochettino ya ce kawo batun komawar Kylian Mbappe Madrid har yanzu jita-jita ce. (Metro)

Ita kuwa Everton ta nemi Barcelona da ta sayar mata da mai tsaron bayanta Samuel Umtiti kafin a rufe kasuwa. (Express, via Goodison News)

Jaridar A Bola ta ruwaito cewa an ga dillalan yan wasan Manchester United a wasan sahre fagen zuwa gasar zakarun Turai da a ka yi a Portugal tsakanin Benfica da PSV Eindhoven. (A Bola - in Portuguese)

Jaridan Gianluca di Marzio ta Italiya ta ce an shirin yiwa dan wasan Watford da Nigeria Isaac Success gwaji a Udinese. (Gianluca di Marzio)

A wata mai kama da haka kuwa Watford din ta sanar da Liverpool cewa dan wasan gabanta Ismaila Saar ba na sayarwa bane. (Watford Observer)

Read full article