You are here: HomeAfricaBBC2021 10 31Article 1391971

BBC Hausa of Sunday, 31 October 2021

    

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallon kafa: Makomar Kroos, Ramsey, Ten Hag, Jovic, Van de Beek, Barnes

Antonio Conte, tsohon kocin Inter Milan Antonio Conte, tsohon kocin Inter Milan

Newcastle na sha'awar dan wasan tsakiya na Real Madrid da Jamus Toni Kroos mai shekara 31. (El Nacional)

Kungiyar ta Pemier ba ta damu da yawan albashin da Aaron Ramsey yake bukata ba a shirin da take na sayo dan wasan na tsakiya dan Wales, mai shekara 30 daga Juventus a watan Janairu. (Tuttosport, daga Mirror)

Haka kuma kungiyar ta Newcastle ta na son kociyan Ajax Erik ten Hag ya zama sabon mai horad da 'yan wasanta amma kuma tana fuskantar kalubalen yadda za ta shawo kansa ya yarda. (Mirror)

Liverpool na duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na Real Madrid da Serbia Luka Jovic, mai shekara 23. (Fichajes)

Liverpool za ta bar mai tsaron ragarta dan Jamus Loris Karius, mai shekara 28, ya tafi a kyauta a watan Janairu- rabonsa da tsare ma ta raga tun 2018. (Mirror)

Tottenham na fuskantar gogayya daga Bayern Munich kan zawarcin dan wasan gaba na Nantes Randal Kolo Muani wanda take son dauka a karshen kakar nan. Dan gaban dan Faransa mai shekara 22, zai kasance ba shi da kungiya a lokacin bazara. (Foot Mercato - in French)

Abokan Donny van de Beek a Manchester United suna ba dan Holland din mai shekara 24, shawara a kan ya sauya wakili domin ya samu damar barin Old Trafford. United ta tattauna da Everton da Wolves kan daukarsa aro. (Mail)

Liverpool na matukar sha'awar sayen dan wasan gaba na gefe na Leicester da Ingila Harvey Barnes, mai shekara 23. (Fichajes)

Tottenham ta bi sahun Leeds a kokarin sayen dan wasan gaba na Espanyol kuma dan Sifaniya Raul de Tomas, mai shekara 27. (Sport Witness daga TEAMtalk)

Crystal Palace za ta katse aron da ta karba na dan wasan gaba na Jean-Philippe Mateta a watn Janairu. Dan Faransan mai shekara 24 yana zaman aro ne daga Mainz har zuwa karshen kakar nan, to amma kuma bay a cikin tsarin kociyan kungiyar Patrick Vieira. (Sun)

Antonio Conte ba ya son karbar aikin horad da kungiya a tsakiyar kaka. Ana danganta tsohon kociyan na Chelsea da Inter Milan da aikin Manchester United da Newcastle United. (Todofichajes)

Derby na son sayar da mai tsaron ragar Scotland David Marshall, mai shekara 36, a watan Janairu. (Sun)

Read full article