You are here: HomeAfricaBBC2022 05 26Article 1546421

BBC Hausa of Thursday, 26 May 2022

    

Source: BBC

Kisan Harira: Abin da Buhari ya ce kan kashe mai ciki da 'ya'yanta hudu a Anambra

Shugaba Muhammadu Buahri Shugaba Muhammadu Buahri

Shugaba Muhammadu Buhai na Najeriya ya gargaɗi ƴan ƙasar da su guji gaggawar mayar da martani ko ɗaukar mataki, ko jawo fargabar da za ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi, sakamakon yaɗuwar bidiyo dabam-dabam na kisan ƴan arewa a kudu maso gabashin Najeriya, da ake zargin ƙungiyar IPOB da aikatawa.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa Buharin kan yaɗa labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ƙara da cewa "a yayin da hukumomin da suka ƙware ke ƙoƙarin gano gaskiyar zarge-zargen da ke ƙunshe cikin hotuna masu ɗaga hankalin da ake yaɗawa, muna kira ga dukkan ƴan ƙasa da su guji gaggawar ɗaukar matakan da za su ƙara rikita al'amarin, sannan su bi doka ta hanyar barin hukumomi yin abin da ya dace.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma gargaɗi jama'a kan su guji yaɗa abubuwan da ba su da tabbas a kan sahihancinsu a shafukan sada zumunta, don durƙusar da masu burin son ganin an samu rarrabuwar kawuna da jawo rikici.

A ƙarshe shugaban ƙasar ya yi tur da Allah-wadai da "kisan gilla da ake yi wa mutanen da ba su ji ba su gani ba" a Kudu maso Gabashi da ma sauran sassan ƙasar.

Ya bayyana irin waɗannan kashe-kashe a matsayin "masu matuƙar ɗaga hankali", tare da gargaɗin masu aikata hakan da cewa su tsammaci tsattsauran martani daga jami'an tsaro.

Read full article