You are here: HomeAfricaBBC2022 03 12Article 1488797

BBC Hausa of Saturday, 12 March 2022

    

Source: BBC

Klopp: 'Salah na da zabi kan kamomarsa a Liverpool'

Kocin Liverpool Klopp tare da Mohamed Salah Kocin Liverpool Klopp tare da Mohamed Salah

Kocin kungiyar Liverpool Jurgen Klopp y ace a yanzu zabi na ga Muhammed Salah na ko zai rattaba hannu kan kwantiragin tsawaita zaman sa a kungiyar ko akasin hakan.

A halin da ake ciki dai kwantiragin Salah zai kare ne a karshen kakar badi.

A baya-bayan nan dan wasan mai shekara 29, ya ce ya na son ci gaba da zama a kungiyar, amma makomarsa na hannun kungiyar kuma baya neman wani gagarumin abu.

"Tabbas Mo ya na sa ran kuluf din zai nuna dogon buri akan shi, mun kuma yi duk wani abu da ya dace don haka, dabara ta rage ga mai shiga rijiya, kuma daman haka ake yi, babu wani abu da ya rage ayi ko wani abu da zan fada amma komai na tafiya yadda ya dace" in ji Klopp.

Klopp ya kara da cewa shi a ganinsa, matakin da kungiyar ta dauka na barin Sala ya zabi abin da ya ke so shi ne ya dace.

"A gani na, wannna shi ne abin da ya dace a halin yanzu. Babu wani abu na daban da ya faru, dan haka ba a rattaba hannu kan wani kwantiragi ba, kuma ba a ki yin hakan ba, babu kuma wanda ya hana Mo yin abin da ya ke so. Shi ya sa na ke cewa babu gaggawa a cikin lamarin nan, mu dakata zuwa lokacin da ya dace."

A shekarar 2017 ne Salah ya shiga kungiyar ta Liverpool daga kulup din Roma na Italiya, kawo yanzu ya zura kwallo 152 cikin wasanni 237 da ya bugawa kungiyar.

Ya taimakawa kuluf din daukar kofin Premier League, da Champions League, da League, sannan ya yi nasarar dauko kofin duniya da na Uefa Super Cup a lokacin da ya ke Anfield.

Read full article