You are here: HomeAfricaBBC2023 05 02Article 1759463

BBC Hausa of Tuesday, 2 May 2023

    

Source: BBC

Ko Barcelona za ta yi wa Osasuna gida da waje a La Liga

Robert Lewandowski Robert Lewandowski

Barcelona da Osasuna za su kece raini a wasan mako na 33 a La Liga ranar Talata a Camp Nou.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 79, ita kuwa Osasuna mai maki 44 tana ta tara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Ranar 9 ga watan Nuwambar 2022, Barcelona ta je ta ci Osasuna 2-1 a wasan farko a kakar bana da suka kara.

David Garcia ne ya fara ci wa mai masaukin baki, Osasuna kwallo a minti na shida da take leda.

Daga baya Barcelona ta zare ta hannun Pedri a minti na uku da komawa zagaye na biyu, sannan Raphinha ya ci na biyu, saura minti biyar a tashi wasan.

A karawar ce aka bai wa 'yan wasan Barcelona biyu jan kati, wato Robert Lewandowski da kuma Gerrard Pigue, wanda ke zaune a benci.

Osasuna ta yi nasara a kan Barcelona a 2020, amma aka doke ta 4-0 a kaka biyu a jere da ta je Camp Nou.

'Yan wasan Barcelona da za su kara da Osasuna:

Ter Stegen, R. Araujo, Sergio, O. Dembélé, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Iñaki Peña, Christensen da kuma Marcos A.

Sauran sun hada da Jordi Alba, Kessie, F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Gavi, Pablo Torre, Arnau Tenas da kuma Lamine Yamal.