You are here: HomeAfricaBBC2023 05 21Article 1771007

BBC Hausa of Sunday, 21 May 2023

    

Source: BBC

Ko ya kamata a ɗauki mataki kan masu amfani da 'filta' wajen ɗaukar hoto?

Yadda ale sauya yanayin hotuna Yadda ale sauya yanayin hotuna

Mutane da dama sun daɗe suna guna-guni kan batun yadda ake sauya yanayin hotuna a kafofin sada zumunta, amma ganin cewa yanzu kimiyyar ta bunkasa zuwa ga bidiyo, to lokaci ya yi da hukumomi za su dauki mataki?

Krystle Berger, ta haƙiƙance cewa ba wai sauya kamanninta take yi gaba ɗaya ba idan ta ɗora hotuna da bidiyo a kan kafofin Instagram da TikTok da Facebook ‘ kawai ina ɗan ƙara yi ma fuskata kwalliya ne da ɗan ƙara mata haske a na’urance’ A cewar ta.

Matashiyar uwa, ‘yar asalin Jihar Indiana, Ms Berger na biyan kuɗi domin ta yi amfani da wata manhaja mai suna FaceTune wadda mutane fiye da milyan 200 ke amfani da ita a duniya.

Manhajar na bai wa masu amfani da ita damar su yi wasu ƴan sauye-sauye a yanayin fuskarsu, kamar ɓoye tamojin fuska, ko kuma suna iya sauya kamanninsu baki ɗaya.

Misali, suna iya rage faɗin fuskokinsu, ko su sauya yanayi da kuma girman idanunsu, ko kuma su yi ma kansu aiki a kan hanci a na’urance.

Da farko manhajar na aiki a kan hotuna ne kawai, amma shekaru biyu da suka wuce FaceTune ya ƙaddamar da wani sabon samfuri da ke iya yin aiki kan gajerun bidiyo, kuma sun kara bunkasa aikinsa.

Har-ila-yau akwai wani manhaja da ke baiwa ma su amfani da shi sauya yanayin hotunan da ke kafofin sada zumunta- Perfect365-za su kaddamar da samfuri mai aikim a kan bidiyo cikin shekaran nan..

Kamfanin ‘yan asalin kasar Isra’ila mai sun a Lightricks ke da manhajar FaceTune kuma shekara biyu da su ka wuce kamfanin na da darajan dala biliyan 1.8’

Mai kamfanin Lightricks, Zeev Farbman ya ce sun a kokarin tabbatar da cewa mahajar na iki cikin sauki. “Za ka so ka baiwa mutane kashi 80 na ‘yancin yin abin da su ke so amma da kashi 20 na wahalar amfani da manhajar. Wasan da mu ke son mu buga ke nan.

Amma an dade ana takaddamar cewa wadannan maanhajojin na da illa, a inda su ke nuni da wani irin kyau na karya wanda ke iya jawo hadari, musamman tsakanin yara da matasa. Misali kashi 80 na ‘yan mata sun ce tun sun a shekara 13 su ke fara sauya yanayin hotunan su, Wannan sakamakon wani bincike ne da Kamfanin kula da fata ta dove ta gudanar a shekarar 2021.

A inda babu wanda ke kira da a haramta amfani da wannan kimmiyar, akwai yunkuri da a ke yin a tilastawa masu tallace-tallace da kuma fada a ji a kafofin sada zumunta wadanda a kan biya su don su yi talla, da su yi bayani idan sun yi amfani da kimmiyar sauya yanayin hotunan su.

A shekarar 2021, kasar Norway ta kaddamar da wata doka da ke tilastawa wadanann bangarorin biyu da su yi bayani idan har an sauya yanayin hoto. Kasar faransa kuma nab iye da ita amma it ana ta dokar ta shafi har da bidiyo.

Birtaniya ma ta na duba lamarin, a inda kudurin gwamnati na tabbatar da tsaro a yanan gizo ke gaban majalisar dokoki. Amma babu tabbas ko dokar za ta shafi ma su talla ne kadai ko kuma har da ma su gfada- a- ji.

Wanin Kakakin ma’aikatar kimiya da fasaha ya ce ” gwamnati na sane da irin hadarin da ke tattere da wannan kimmiyar ke da ita, kuma ta dauki lamarin da matukar muhimmanci.

Wani dan majlisa Luke Evans ya dade y ana yakin neman masu talla da kuma fada a ji a kafofin sada zumunta da su yi bayani idan har sun san cewa sun sauya fasalin hotunan da su ka yi amfani da su.

Ya na son ya ga cewa dokar ta kunshi tsarin da zai shafi har da bidiyo da kuma wadansu kimiyan da za su taso.

“Ya na da muhimmanci mu wayar da kai kan bayyana Gaskiya cikin abin da ya shafi wannan kimmiyar.” A cewar sa. “A gani na wannan Magana ce ta Gaskiya”

Read full article