You are here: HomeAfricaBBC2023 07 01Article 1795934

BBC Hausa of Saturday, 1 July 2023

    

Source: BBC

Kotun Ƙolin Brazil ta haramta wa tsohon shugaban ƙasar riƙe mukami

Tsohon shugaban kasar  Brazil, Jair Bolsonaro Tsohon shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro

Tsohon shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, ya bayyana hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da shi daga rike mukamin gwamnati har zuwa 2030 a matsayin cin amana.

Kotun ta same shi da laifin yin amfani da karfin ikonsa na shugaban kasa zamanin da yake mulki.

A yayin wanijawabi da ya yi ne wanda aka yada ta talabijin a watan Yuli na bara, inda a lokacinya nuna shakku kan sahihancin tsarin zaben kasar ta hanyar kwamfuta ba tare da ya nuna wata sheda mai karfi ta zargin magudi ba.

Mista Bolsonaro ya ce yana tunanin daukaka kara, kuma zai ci gaba da fafutukar neman 'yancin Brazil.

Bayanai na nuna cewa mai yiwuwa matarsa Michelle Bolsonaro ta tsaya takara a zaben gaba, sannan yana da 'ya'ya uku duka 'yan siyasa, wadanda suma za su iya shiga rigarsa.

An kama shi ne da laifin makarkashiya ga dimukuradiyya, bayan ya nuna shakku kan sahihancin zabukan kasar.

Mafi rinjayen alakalan kotun sun ayanna kalaman nasa a matsayin babban laifi ga dimukurdaiyyar kasar.

Dimukuradiyyar da aka mayar da ita kasar a tsakiyar shekarun 1980, bayan gomman shekarun mulkin soja.

Daya daga cikin jam'iyyun da ke hamayya da jam'iyyar tsohon shugaban ne

A kasar wadda take da rabuwar kai sosai a tsakanin magoya bayan shugaban kasar mai ra'ayin kawo sauyi Luiz Inacio Lula da Silva, magoya bayan shugaban mai ci a yanzu, sun rika yi wa tsohon shugaban, Bolsonaro, wanda ya taba cewa ba wanda ya isa ya kawar da shi daga mulki idan ba Allah ba.

Read full article