BBC Hausa of Tuesday, 4 July 2023
Source: BBC
Leed United ta ɗauki tsohon kocin Norwich Daniel Farke a matsayin sabon kocinta na tsawon shekaru huɗu.
Dan ƙasar Jamus ɗin mai shekara 46 ya shafe shekaru huɗu a Norwich kuma sai da ya kai ta Premeir sau biyu.
Farke ya yi kakar bara ne a ƙungiyar Jamus ta Borussia Monchengladbach amma an kore shi bayan sun ƙare kakar a matsayi na 10.
Leeds ta faɗa gasar Championship daga Premier 2022-23 bayan sun kori koci biyu a kakar, suka ƙarasa ta da Sam Allardyce.
A watan Yunin 2017 ne aka naɗa Farke a matsayin kocin Carrow Road, ya ɗauki Norwich ta ƙare a matsayi na biyu bayan ragamarta da ya ja.
Amma shekara mai zuwa sai suka ƙare a matsayi na ƙarshe a Premier amma duk da haka Farke ya sake dawowa da su Premier.
Bayan gaza ƙoƙari a wasan Premeir 2021-22 an kore shi a watan Nuwamba - awanni bayan sun sha kashi a Brentford.
Farke ya koma wata ƙungiya a Rasha bayan nan, amma ya bar ƙungiyar ne sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin Rasha da Ukraine.
Leeds za ta fara wasan gasar Championship na wannan kakar a gida da Cardiff a ranar Lahadi 6 ga watan Agustan mai zuwa.