BBC Hausa of Sunday, 2 July 2023
Source: BBC
Liverpool ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar RB Leipzig Dominik Szoboszlai kan kuɗi yuro miliyan 70.
Dan wasan ya sanya hannu ne kan kwantaragin shekara biyar.
Liverpool ba ta bayyana wasu tsarabe-tsarabe ba da ke tsakaninsu da ɗan wasan Hungary ɗin wanda shi ne ɗan wasa na biyu da suka ɗauka a bana.
Szoboszlai zai isa Liverpool ne idan ya samu izinin aiki a ƙasar.
Ƙungiyar ta ɗauki ɗan wasan Argentina Alexis Mac Allister daga Brighton.
"Ƙungiya ce da ke da daɗaɗɗen tarihi, akwai 'yan wasa masu kyau, ga koci mai kyau," in ji shi.
"A wajena mataki ne mai kyau koma wa irin waɗannan ƙungiyoyi. Magoya bayansu cike suke da alfahari, filin wasanma haka, komai na ƙungiyar ya yi."
Ɗan wasan mai shekara 22, ya lashe kofin Jamus a kaka biyu da ta wuce baya.
Szoboszlai ya yi wasan 31 a Bundesliga a bara, ya ci kwallo shiga ya kuma bayar da kwallo takwas an ci.
Ya sanya hannu daga ƙungiyar Austrian Red Bull Salzburg a watan Janairu 2021, ya ci kwallo 2o ya bayar da 21 an ci a wasa 91 da ya buga.
Kwantaragin Szoboszlai ta ƙare ne a ranar Juma'a amma Liverpool ta yi maza ta ɗauki matakin sanya hannu da shi a matakin ta da shi.
Kocin ƙungiyar Jurgen Klopp na neman yadda zai ƙarfafa tsakiyar tawagarsa bayan da 'yan wasa irin su James Milner da Naby Keita da kuma Alex Oxlade-Chamberlain suka bar ƙungiyar.