You are here: HomeAfricaBBC2023 04 17Article 1750457

BBC Hausa of Monday, 17 April 2023

    

Source: BBC

Luis Enrique ya yi takaicin rashin jagorantar Chelsea, Arsenal na zawarcin Vlahovic

Luis Enrique Luis Enrique

Chelsea ta gana da tsohon manajan Bayern Munich Julian Nagelsmann, a kokarin da suke ni na neman gwarzon shugaba, bayan korar Graham Potter. (Times - subscription required)

Tsohon manajan Sifaniya Luis Enrique, bai ji dadi ba kan rashin nasarar jagorantar Chelsea gabannin kungiyar ta kai bantenta a wasan gab da na karshe na gasar Champions League bayan lallasa Real Madrid, Sai dai ana samun rahotannin zai iya taimakawa wajen dauko dan wasan Barcelona kuma na tsakiyar Sifaniya mai shekara 18 wato Gavi. (AS - in Spanish)

Real Madrid na son amfani da dama wajen dauko dan wasan tsakiya na Manchester City Erling Haaland, domin dauko mai kai harin na Norway a shekarar 2024.(Fichajes - in Spanish)

Arsenal na yunkurin dauko dan wasan Juventus, Dusan Vlahovic mai shekara 23, da kuma dan wasan Everton na tsakiyar Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 26,a matsayin kar ta kwana idan ba su samu damar daukar dan wasan Sabiyan. (Football Insider)

Dan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, zai fi son ci gaba da zama a Borussia Dortmund, tare da nazarin yadda za ta kaya daga nan zuwa shekarar 2024, kafin daukar matakin inda zai nufa nan gaba. (Times - subscription required)

Tsohon mai kai hari na Liverpool Robbie Fowler ya yi amanna Reds na da 'yancin kashe yawancin kudaden da suka ware na sayan 'yan wasa akan Bellingham a kakar nan, saboda su na matukar bukatar zakakurin dan wasa kamar shi. (Mirror)

Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen na magana da Manchester United, sai dai dan wasan na Najeriya mai shekaru 24 ya bayyana karar ya na jin dadin zama a kulub din Italiyan.(TG5, via Manchester Evening News)

Manajan Manchester City, Pep Guardiola na kokarin ganin dan wasan tsakiya na Jamus Ilkay Gundogan, mai shekara 32 bai bar kulub din ba. Ya na irin wannan kokarin kan tsohon dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 28, duk da cewa duka 'yan wasan biyu ana rade-raden su na son koawa wani kulub din. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Jamus Toni Kroos ya shirya ci gaba da zama a Real Madrid har wata kakar wasan, masi shekara 33, ya amince da sabunta kwantiraginsa a kulub din. (Marca)

Read full article