BBC Hausa of Monday, 26 June 2023
Source: BBC
Luka Modric ya sanya hannu kan sabuwar kwantaragi a Real Madrid ta tsawon shekara guda, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a ƙungiyar har nan da 2024.
Ɗan wasan tsakiya na Croatia wanda kwantaraginsa ya kamata ta ƙare a bana, an ta jin bayanan cewa yana shirin komawa gasar kwallon kafa ta Saudiyya da ake kira Saudi Arabia Pro League.
Modric mai shekara 37, ya bugawa Real wasa 488, ya ci La Liga uku da Champions biyar tun bayan komawarsa ƙungiyar daga Tottenham a 2012.
A 2018, Modric ya ci kyautar Ballon d'Or lokacin da ƙasarsa Crotia ta je wasan ƙarshe a gasar cin Kofin Duniya.
Bayan sanarwar da aka fitar kan sabuwar kwantaragin nasa a Madrid babban birnin Sifaniya, Modric ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa " Gida daɗi Gida daɗi".
Ya bi sawun 'yan wasa irinsu Toni Kroos da Dani Ceballos da kuma Nacho Fernandez wajen tsawaita kwantaraginsu a ƙungiyar a bana, kuma har yanzu ana musu kallan manyan 'yan wasan ƙungiyar da ta lashe gasar Zakarun Turai sai 14.
Tuni Real ta ɗauki babban ɗan wasan tsakaiya na Ingila daga kungiyar Borussia Dortmund domin ƙarawa tsakiyarta ƙarfi da kuma gogayya tsakanin yan wasanta.