BBC Hausa of Sunday, 21 May 2023
Source: BBC
Carlo Ancelotti ya ce La Liga tana da matsalar kalaman wariya, bayan da aka ci zarafin Vinicius Junior a Valencia ranar Lahadi.
An bai wa dan kwallon Brazil, mai shekara 22 jan kati a minti na 97, bayan cacar baki mai zafi da shi da Hugo Duro.
Tun farko an ja hankalin alkalin wasan, domin ya umarci magoya bayan Valencia su dakatar da kalaman wariya da suke yi wa dan kwallon Real Madrid din.
''Wannan abin da muka gani ba abin da za mu amince bane. Gabaki dayan filin wasa na rera kalaman wariya,'' kamar yadda Ancelotti ya sanar da Movistar Plus.
''Bana son yin magana a kan kwallon kafa a yau din nan, ba wani amfani a yi magana kan tamaula. Na sanar da alkalin wasan da ya kamata ya tsayar da karawar.''
''La Liga tana tare da babbar matsala. Ni a waje na Vinicius dan kwallo ne mai mahimmaci a duniya. Ya kamata a dakatar da wannan halayyar a lokacin wasanni.
Vinicius, wanda karon farko kenan da aka yi masa jan kati a tarihin sana'arsa ta taka leda, ya fuskanci kalaman wariya da na cin zarafi karo da dama a La Liga a kakar nan.
An dan dakatar da karawar a zagaye na biyu, bayan da dan kwallon Real ya nuna bacin ransa kan kalaman wariyar da ake rerawa.
Daga lokacin ne ransa ya baci har ta kai da aka yi masa jan kati a fafatawar da aka ci Real 1-0, karo na takwas da ta yi rashin nasara a La Liga a bana.
Ita kuwa Valencia, wadda ta ci wasan ta yi sama zuwa ta 13 da tazarar maki biyar tsakaninta da 'yan ukun karshen teburin La Liga.