You are here: HomeAfricaBBC2023 07 03Article 1796705

BBC Hausa of Monday, 3 July 2023

    

Source: BBC

'Maimakon su cece mu sai suka kifar da jirginmu'

Hoton alama Hoton alama

Mutum huɗu da suka tsira daga kifewar jirgin ruwa na baƙin-haure a kusa da gaɓar ruwan Girka sun bayyana cewa matakin da masu gadin teku na Girka suka ɗauka ne ya haddasa kifewar jirgin da ke cike maƙil da mutane.

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi ƙiyasin cewa aƙalla mutum 750 ne suka mutu, akasarinsu 'yan Pakistan, bayan jirgin ya nitse da su a ranar 14 ga watan Yuni.

Lamarin na cikin bala'o'i mafiya muni da aka taɓa gani a Tekun Baharrum - mutum 104 ne suka tsira da rayukansu kuma aka tsamo gawa 80.

Ba za mu fadi sunayen mutanen huɗu na gaskiya ba saboda tsaron lafiyarsu, amma mun iya tantance ko su wane ne ta hanyar majiyoyi fiye da ɗaya.

Wasu daga cikin mutanen da suka yi magana da BBC ta waya na tsare ne a sansanin 'yan gudun hijirar Malakasa mai nisan kilomita 40 daga babban birnin Girka Athens, yayin da wasu kuma suka bar sansanin a yanzu.

Ba a barin 'yan jarida shiga sansanin, wanda aka zagaye da waya.

'Sun zabaro jirgin ta ciki'

"Mun zaci za su [masu gadin teku na Girka] cece mu ne amma sai suka kifar da jirgin," kamar yadda ɗan Masar ya faɗa wa BBC.

Ya ce dakarun na jan jirgin da igiya loakcin da ya kife a daidai ɗaya daga cikin wuri mafi zurfi a tekun na Baharrum, kusan kilomita 80 daga gaɓar ruwan Girka.

Da farko hukumomi a Girka sun ƙaryata batun, suna masu iƙirarin cewa lokacin da suka yi yunƙurin ɗaura igiya a jikinsa don tantance abin da ke faruwa sai fasinjojin suka kwance kuma suka ce za su wuce zuwa Italiya ne.

Amma wani ɗan Syriya da ya tsira ya faɗa mana: "Sun ja jirgin da igiya ta cikinsa kuma suka zura a guje."

Wannan labarin ya yi daidai da wanda ɗan Masar ya bayar, wanda ya ce masu gadin "fizgarmu suka yi kuma suka sa jelar jirgin ta nitse".

Wasu da muka yi magana da su sun faɗa mana cewa hukumomin Girka sun umarce su da kada su yi magana da 'yan jarida game da yadda dakarun tsaron tekun suka yi yunƙurin ceto jirgin nasu, amma idan sun yi maganar to kada su zargi jami'an tsaron na Girka.

Ɗaya daga cikinsu ya ce hukumomi sun matsa masa don ya sauya labarin da ya bayar na yadda lamarin ya faru "za su ba shi tallafin kuɗi a madadin haka kuma za a hanzarta ba su takardun matsayin 'yan gudun hijira".

'Dabara mai haɗari'

Mun nemi jin ta bakin jami'an tsaron na Girka game da labarin da mutanen suka ba mu, amma sun ce ba za su ce komai ba saboda duk abin da suka ce zai iya shafar binciken da hukumomi ke yi kan lamarin.

Sun kuma ce mu duba wata sanarwa da suka fitar, wadda ta musanta batun cewa su suka ja jirgin, da kuma cewa ba a kai wa mutanen ɗauki ba duk da kiraye-kirayen da suka dinga yi.

Ƙungiyar Sea-Watch mai mazauni a Jamus kan hayi jiragen ruwa don ceto baƙin-haure a ruwan na Baharrum. Ta ce ba ta da cikakkun bayanin da za ta tabbatar da abin da ya faru.

Amma shugaban sashen ayyukanta ya faɗa mana: "Jan tsohon jirgi da igiya ɗauke da ɗaruruwan mutane a babban teku tabbas abu ne da ba zai yiwu ba kuma zai haddasa bala'i."

"Abin da muika fahimta daga hotunan da muka gani da kuma labaran da muka samu, bai dace a yi yunƙurin ceto mutane ba daga jirgin da ke shirin kifewa."

Mr Hahn ya ce jan jirgi da igiya abu ne haɗari amma za a iya yin hakan a wasu lokuta.

Biyu daga cikin waɗanda suka tsira sun ce an nemi su ba da hujja a kan mutum tara 'yan Masar da ake zargi da yin safrarar mutane.

Amma duka mutum huɗun sun ce 'yan Masar ɗin fasinjoji ne, zaune a cikinsu yayin tafiyar. Suka ce direbobin jirgin sun rufe fuskokinsu kuma ba su fiya fitowa daga ɗakin tuƙi ba.

"Wasu daga direbobin sun afka ruwa lokacin da suka ga jami'an tsaron amma wasu daga cikin 'yan Masar ɗin ne suka yi ƙoƙarin ci gaba da tuƙawa," a cewar ɗaya daga cikinsu. "A ganina ba su ne suke safarar mutane ba."

Wasu 'yan Masar da ke fargabar 'yan uwansu na cikin jirgin sun faɗa wa BBC cewa sun biya wa kowane mutum ɗaya dala 4,500 (kusan naira miliyan uku da rabi) don tafiyar.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta UNHCR ta yi murna da ƙaddamar da bincike kan abin da ya faru kuma ta yi kira da "matakin gaggawa don kauce wa ƙarin mace-mace".

Alƙaluman UNHCR sun nuna cewa mutum 80,000 ne suka tsallaka Baharrum zuwa Turai zuwa yanzu a shekarar nan, inda aka ƙiyasta 1,200 sun mutu ko sun ɓace a kan hanya.

Read full article