You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798580

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

    

Source: BBC

Man City na son £50m kan Silva, Arsenal na gab da saye Rice kan £105m

Bernardo Silva Bernardo Silva

Manchester City ta shirya karban tayin da aka gabatar na tsakanin fam miliyan 45 zuwa fam miliyan 50 kan ɗan wasan Portugal, Bernardo Silva mai shekara 28. (Football Insider)

Newcastle United na son saye ɗan wasan Ingila Marc Guehi, mai shekara 22, duk da cewa Crystal Palace na taya shi kan fam milyan 60. (Football Insider)

Thiago Alcantara ya ja hankalin kungiyoyin ketare, ciki harda Saudiyya, ko da ya ke Liverpool a hukumance bata karɓi kowanne tayi kan ɗan wasan mai shekara 32 ba. (Times - subscription required)

Arsenal na gab da cimma burinta na tayi fam miliyan 105 da ta gabatar kan ɗan wasan tsakiya Declan Rice, mai shekara 24 daga West Ham.(Guardian)

Kungiyoyin Arsenal, Manchester City, Manchester United da Tottenham na cikin jeren masu farautar ɗan wasan Red Bull Salzburg Oscar Gloukh, mai shekara 19. (Guardian)

Manchester United na harin mai tsaron raga na Brighton Robert Sanchez, mai shekara 25. (Mail)

Barcelona ta amince da yarjejeniyar sayen Vitor Roque daga Athletico Paranaense amma tana son ganin ko za ta iya rage albashinsa kafin ya dawo kungiyar a Janairun badi. (Sport - in Spanish)

Real have ta bukaci Inter Milan ta faɗi nawa za ta sayar da ɗan wasanta asalin Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 25. (Sport - in Spanish)

Brighton ta sake gabatar da zawarcinta kan ɗan wasan Ajax asalin Najeriya Calvin Bassey, mai shekara 23. (The Athletic - subscription required)

Almeria ta ce Everton da wasu kungiyoyin Italiya biyu sun gabatar da tayi kan dan wasanta asalin Mali El Bilal Toure, mai shekara 21. (Diario de Almeria - in Spanish)

Ɗan wasan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 22, ya yanke shawarar barin Chelsea, AC Milan na son daidaitawa da shi. (Metro)

Ɗan wasan Southampton Tino Livramento zai so ya koma Newcastle bayan Chelsea ta nuna alamun neman sake dauko shi. (Mail)

Arsenal ta shirya sayar da Folarin Balogun a wannan kaka kan £50m. (Mirror)

Arsenal ta shirya amince da tsawaita zaman William Saliba, mai shekara 22, zuwa 2027. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan Newcastle Allan Saint-Maximin, mai shekara 26, ya kasance na baya-bayanan da Suadiyya ke zawarci.(90min)

Al-Ettifaq na son sabon kocinta Steven Gerrard ya yi kokarin cimma yarjejeniya da Scott Wright, mai shekara 29. (Football Insider)

Aaron Ramsey ya tattauna da Cardiff kan sake komawa Wales, ɗan wasan mai shekara 32 kwangilarsa ta kare da Nice. (Talksport)

Read full article