You are here: HomeAfricaBBC2023 04 28Article 1757195

BBC Hausa of Friday, 28 April 2023

    

Source: BBC

Man U ta ce ba za ta yi doguwar ja-in-ja a kan Kane ba, Liverpool na iya kashe maƙudan kuɗi a kan Nicolo

Harry Kane Harry Kane

Manchester United na son ɗaukar ɗan ƙwallon Ingila mai kai hari, Harry Kane, amma za ta iya juya baya ta duba sauran zaɓin da take da su, a kan ta shiga dogon cinikin ɗan wasan mai shekara 29 da Tottenham (Star)

United na sha'awar ɗauko golan Dinamo Zagreb ɗan ƙasar Croatia, Dominik Livakovic, mai shekara 28, saboda kwanturagin da take da shi da zaɓinta na farko, David de Gea yana ƙarewa a wannan bazara. (Jutarnji, via Football 365)

Mauricio Pochettino ba zai yi amfani da ejan ba, a lokacin tattaunawa kan ingantattun bayanan aikin da zai karɓa a matsayin kocin Chelsea na gaba . (Telegraph )

Chelsea tana sa ido a kan golan Sifaniya, David Raya da kuma ɗan wasa mai kai hari na Ingila Ivan Toney, dukkansu 'yan shekara 27, don ɗaukar su a lokacin bazara daga Brentford. (Football London)

Chelsea na shirin ganawa da Inter Milan don tattauna makomar ɗan wasa mai kai hari daga ƙasar Belgium, Romelu Lukaku, ɗan shekara 29 wanda yanzu yake zaman aro a kulob ɗin na Serie A, da kuma yiwuwar ɗaukar golan Kamaru, Andre Onana, mai shekara 27. (Evening Standard)

Liverpool na iya kashe kuɗi maƙudai a kan ɗan ƙwallon tsakiya na Inter Milan daga ƙasar Italiya Nicolo Barella, mai shekara 26, duk da ta ce a kai kasuwa, saboda kuɗin da Borussia Dortmund ta tsuga wa ɗan wasan tsakiyar Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19 a bazarar nan. (Sport Mediaset via Express)

Read full article