You are here: HomeAfricaBBC2022 08 23Article 1608101

BBC Hausa of Tuesday, 23 August 2022

    

Source: BBC

Man United ta huce fushinta a kan Liverpool

Sancho (tsakiya) ya ci kwallo daya a gasar Sancho (tsakiya) ya ci kwallo daya a gasar

Manchester United ta yi nasarar doke Liverpool da ci 2-1 a wasan mako na uku a gasar Premier League da suka kara ranar Litinin a Old Trafford.

United ta fara cin kwallo ta hannun Jadon Sancho minti shida da fara tamaula, haka suka je hutu da kwallo daya a ragar Liverpool.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne United ta kara na biyu ta hannun Marcus Rashford, wanda sai da VAR ta tantance, bayan da aka dauka ya yi satar gida.

Mohamed Salah ne ya zare kwallo daya na 10 da ya ci United, ya zama na farko a Liverpool da ya 10 a kungiyar Old Trafford.

Tun a baya United ba ta taba rashin nasara a Premieer League ba a karawa 20 a hannun Liveerpool idan har ita ce kan gaba a cin kwallo a wasa 17 da canjaras uku.

Ba wanda ya hangi cewar United za ta doke Liverpool, domin wasa daya ta yi nasara a kan kungiyar Anfield daga fafatawa 12 baya, tun kan haduwar ta ranar Litinin.

Inda kungiyar Old Trafford ta sha kashi a wasa biyar da canjaras shida.

Ba a fara karawar da Cristiano Ronaldo ba, inda United ta ci wasa kaso 17 cikin 100 idan bai fara wasa ba, idan ka kwantanta da kaso 50 cikin 100 da ta yi nasara idan ya fara buga mata tamaula.

United ta gabatar da sabon dan wasanta Casemiro, wanda ta dauka daga Real Madrid a bana.

Dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 30 ya ce ya koma daya daga babbar kungiya a fannin tamaula a duniya, bayan kaka tara a Real Madrid.

United ta sayi dan wasan kan fam miliyan 70, kan yarjejeniyar kaka hudu, wanda zai zama kan gaba a karbar albashi a Old Trafford.

Bayan da ya koma Sifaniya da taka leda daga Sao Paulo a 2013, Casemiro ya dauli Champions League biyar a Real Madrid da La Liga uku da Cope del Rey daya.

Ya buga Champions League a bara da Real ta doke Liverpool ta lashe kofin Zakarun Turai na 14 jumulla, wanda ya yi mata wasa 336.

Manchester United ta ci wasan farko a kakar bana kenan, bayan da Brighton ta doke ta 2-1 a makon farko da 4-0 da Brentford ta yi nasara a sati na biyu.

Liverpool kuwa ta fara rashin nasara a karawar mako na uku, bayan da ta yi 2-2 a gidan Fulham da 1-1 da ta yi da Crystal Palace a Anfield.

Ranar 27 ga watan Agusta Manchester United za ta je Southampton domin buga wasan mako na hudu a gasar ta Premier League.

A kuma ranar Liverpool za ta karbi bakuncin Bourneemouth a wasan na babbar gasar tamaula ta Ingila.

Read full article