You are here: HomeAfricaBBC2023 07 02Article 1796432

BBC Hausa of Sunday, 2 July 2023

    

Source: BBC

Man Utd ta gagara nasara kan Hojlund, Mata zai bar Turkiyya

Rasmus Hojlund Rasmus Hojlund

An yi watsi da tayin Manchester United na fam miliyan 30, kan ɗan wasan gaba a Atalanta mai shekara 20 asalin Denmark, Rasmus Hojlund. (Corriere dello sport, in Italian)

Shugaban Inter Milan Beppe Marotta ya tabbatar da zawarcin Manchester United kan ɗan wasan Kamaru mai tsaron raga Andre Onana, mai shekara 27. (Mail)

United na kuma sa ido kan ɗan wasan Feyenoord mai tsaro raga, Justin Bijlow, idan ta gaza nasara a cinikin Onana. (Mirror)

Newcastle na dab da cimma yarjejeniya saye ɗan wasan Italiya mai shekara 23 Sandro Tonali daga AC Milan. (Fabrizio Romano)

Real Madrid na fatan doke Barcelona a cinikin ɗan wasan Fenerbahce Arda Guler. Ɗan wasan na Turkiyya mai shekara 18 dole a biya fam miliyan 15 kafin a iya raba shi da kungiyarsa kamar yada aka cimma a kwantiraginsa da sai 2025 zai kare. (Mundo Deportivo - in Spanish)

West Ham ta cire Declan Rice a rukunnin 'yan wasanta da take sayar da rigunansu, yayinda ya ke gab da cimma yarjejeniyar fam miliyan 105 da Arsenal. (Mirror)

Ɗan wasan Chelsea mai shekara 20 Levi Colwill, ana sa ran ya taka rawar gani karkashin sabon koci Mauricio Pochettino duk da cewa yana samun tayi daga Brighton, Liverpool da Manchester City. (Football.London)

Tsohon kocin Sifaniya Spain Juan Mata, mai shekara 35, ya sanar da barin kungiyar Galatasaray ta Turkiyya. (Tribal Football)

Ɗan wasan baya a Ajax da Netherlands Jurrien Timber, mai shekara 22, zai kammala yarjejeniyar komawa Arsenal a mako mai zuwa kan fam miliyanm 45.(Mirror)

Ɗan wasn gaba a Jamus Kai Havertz, mai shekara 24, ya kasance ɗan wasa mafi tsada a Arsenal da za a ke biya albashin fam miliyan 17 a duk shekara bayan komawa kungiyar daga Chelsea. (Bild, via Goal)

Ɗan wasan tsakiya Danny Drinkwater, mai shekara 33, ya ce zai so ya sake komawa Leicester City bayan barin kungiyar zuwa Chelsea a 2017. (SportBible)

Da wuya Manchester United ta daidaita da ɗan wasan Austria Marcel Sabitzer, mai shekara 29, ko ɗan wasan Netherlands mai shekara 30, Wout Weghorst a wannan makon. (Manchester Evening News)

Read full article