You are here: HomeAfricaBBC2021 07 31Article 1321729

BBC Hausa of Saturday, 31 July 2021

    

Source: BBC

Marcus Rashford: Dan kwallon Manchester United zai yi jinyar wata uku

Marcus Rashford, dan wasan Manchester United Marcus Rashford, dan wasan Manchester United

Dan kwallon Manchester United Marcus Rashford zai yi jinyar watanni uku saboda za a yi masa tiyata a kafadarsa a mako mai zuwa.

Dan shekaru 23 din ya dade yana fama da matsala a kafadarsa kuma ana ganin cewa tiyata ce mafita ga matsalar.

Da farko United na jan kafa amma yanzu sun amince a yi wa dan kwallon tiyata.

Rashford ya zura kwallo 11 cikin wasanni 37 a gasar firemiyar kakar wasan da ta wuce kuma yana cikin tawagar Ingila a gasar Euro 2020.

"Bayan tattaunawa tsakanin Marcus da Ole Gunnar Solskjaer da kuma likitocinmu, mun yanke shawarar za a yi masa tiyata ba tare da bata lokaci ba," in ji sanarwar da kungiyar ta fitar.

Rashford ya taimakawa United ta kammala a matsayin kungiyar ta biyu a gasar Firemiyar kakar wasan da ta wuce inda Manchester City ta lashe kofin.

Read full article