You are here: HomeAfricaBBC2023 06 09Article 1783322

BBC Hausa of Friday, 9 June 2023

    

Source: BBC

Masu sayen kayanmu sun janye daga Kano saboda rusau - Ƴan kasuwa

Hoton alama Hoton alama

Harkokin kasuwanci na neman durƙushewa a kasuwar Ƙofar Wambai da ke tsakiyar Kano, saboda rashin tabbas, a cewar wata ƙungiyar 'yan kasuwa.

Wasu 'yan kasuwa a birnin sun ce rushe gine-ginen da gwamnatin jihar ke cewa an yi a filayen da aka mallaka ba bisa ƙa'ida ba, ya yi mummunan tasiri a kan harkokin kasuwancinsu.

Sun ƙara da cewa sanadin wannan lamari "hada-hada a kasuwar ta tsaya cik".

Wani jagora a kasuwar ya shaida wa BBC cewa "Filin Idin nan da ake fakin, (a baya) in ka shigo za ka ga 'yan Nijar, 'yan Kamaru, 'yan Chadi suna shigowa su yi tireloli, amma tun daga ran da abin nan ya faru, ba wani mutum da ya ƙara zuwa ya sayi kaya don ya fita da shi".

Alhaji Sharif Nata’ala Isma’il shugaban gamayyar ƙungiyoyin kasuwar Ƙofar Wambai ya ce bayan rusau ɗin na gwamnatin Kano a Babban Masallacin Idi, wasu ɓata gari sun ɓalle shaguna masu yawa tare da sace musu dukiya da kayan sayarwa.

A cewarsa al'amarin ya haddasa wa 'yan kasuwar gagarumar asarar kuɗi da za su iya kai wa naira biliyan ɗaya.

Ƙungiyar dai ta roƙi gwamnatin Kano ta taimaka ta kai musu ɗauki, saboda a cewarsu har yanzu ana kai musu hari jifa-jifa.

'Yan kasuwar ta Kofar Wambai sun ce abubuwan da suka faru sakamakon rushe wasu gine-gine a masallacin idi sun yi muni sosai.

Alhaji Sharif Nata’ala Isma’il ya ce daga ƙiyasin da suka yi bayan tattara bayanai, ‘yan kasuwar sun tafka asarar miliyoyin naira, al’amarin da ya jefa su cikin fargaba.

Shugaban 'yan kasuwar ya yi iƙirarin cewa gwamnati ta yi rusau ɗin ba tare da kai musu sanarwa, don su kwashe kayansu ba. Ya ce "Shi ya sa da mu da yaranmu da 'yan'uwanmu, Allah ya sani, ba ma iya barci".

Ana fargabar cewa hukumomin jihar za su ci gaba da rusa gine-ginen da suka yi zargin an yi ba bisa ƙa'ida ba hatta a cikin kasuwar ta Ƙofar Wambai.

Gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Ganduje ce ta yanka filayen musamman a cikin Babban Filin Masallacin Idin Kano, wanda ke daura da manyan kasuwannin biyu, sannan ta raba wa wasu mutane, wasu kuma suka saya da kuɗinsu.

Sai dai jam'iyyar NNPP mai mulki a yanzu ta yi ta sukar lamirin wannan mataki tun lokacin da take adawa, kuma ta lashi takobin soke mallakar filayen tare da rushe gine-ginen da ta ce an yi su a filayen gwamnati ko na al'umma.

Mun tuntuɓi sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa game da wannan batu, amma ya ce zai kira daga bisani don yin ƙarin bayani.

Sai dai an sha jin jami'an gwamnatin Kanon na cewa suna aikin rushe wuraren da aka gina "ba bisa ƙa’ida ba ne", da nufin dawo da martabar jihar.

Read full article