BBC Hausa of Thursday, 9 March 2023
Source: BBC
A ranar 18 ga watan Maris ne ‘yan Najeriya za su fita rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri’arsu ga gwamnonin jiharsu a mafi yawan ɓangarorin ƙasar.
A ranar Laraba ne hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗaga zaɓen gwamnonin da aka tsara gudanarwa a ranar 11 ga watan Maris ɗin da muke ciki, bayan kotun ɗaukaka ƙara ta ba ta umarnin sake saita na’urar BVAS mai tantance masu zaɓe.
Cikin ƴan takara 418 da ke neman gwamna a jihohin Najeriya 28, 25 ne kawai mata. Hakan ya nuna an samu raguwar matan da ke takara a bana idan aka kwatanta da waɗanda suka yi takara a 2019.
Mace ɗaya ce take takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, a jihar Adamawa, yayin da jam’iyyar Labour ke da mace ɗaya da ke neman gwamna a jihar Rivers.
Bayan waɗan nan matan 25 akwai mata da yawa da ke a matsayin mataimakan gwamna, mafi shahara su ne yan fim din nan Funke Akindele a Legas da Tonto Dikeh.
A tarihin Najeriya, sau ɗaya mace ta taɓa yin gwamna - Virginia Ngozi Etiaba ta jihar Anambra, ita watanni uku kacal ta yi a ofis.
AbiaLancester-Okoro Nnennaya Ngwamma
Nnennaya Ngwamma ƴar shekara 62 ta kammala karatunta ne a jami’ar Queen Mary da ke Landan a 2007.
Tana takara ne a PRP daga 2019, ta nemi sanata a birnin tarayyar Abuja ƙarƙashin jam’iyyar YPP.
Johnson-Ogbunele Gladys Ikonnaya Ugozika
Johnson-Ogbunele Gladys Ikonnaya Ugozika, na da shekara 58 da haihuwa, tana takara ne a jam’iyyar SDP.
Ta kammala karatunta a kwalejin lafiya ta Nsukka kuma tana aiki ne a matsayin ƙwararriyar likita a Birtaniya.
AdamawaDahiru Ahmed Aishatu
Aisha Dahiru Ahmed Binani tana da shekara 51 da haihuwa, tana kuma neman wannan matsayi ne a jam’iyya mai mulki ta APC, ita kaɗai ce ƴar takara mace a APC, kuma yar takara ɗaya mace a Adamawa.
A yanzu haka sanata ce da ke wakiltar Adamawa ta tsakiya kuma ita ce ke jagorantar kwamitin cimma muradan ƙarni na majalisar dattijai.
Akwa IbomEkanem Abasiekeme Mfonobong
Abasiakeme Mfonobong Ekanem, shekararta 35, ba ta da aure, kuma tana takara ne a jam’iyyar AA a matsayin gwamnan jihar Akwa Ibom.
Ta yi karatunta a jami’ar Uyo kuma tana harkar kasuwanci ita ce ke tafiyar da gidauniyar Sengah Life, wadda ke taimaka wa matan da ke fama da matsalar kansar mama.
Udoh Emem Monday
Mrs Udoh Emem Monday ƴar shekara 43 tana takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar SDP.
Tana aiki a wani kamfanin mai, ƙwararriya ce a fannin tsare-tsaren ci gaba.
Benue Chenge Rosaline Ada
Chenge Rosaline Ada, shekararta 51 tana takara ne a ADP bayan ta yi takara sau biyu a jam’iyyun APC da PDP.
Ta kafa tarihi da dama a matsayinta na mace ta farko da ta zama cikakkiyar injiniya a arewacin Najeriya, Mace ta farko da ta zama babbar manaja ta hukumar ruwa ta jihar Benue kuma ita ce mace ta farko da ta zama shugabar manyan koguna 12 na Najeriya.
Dabo Aduzuana Aondona Sharon Fumi Catherine
Aondona Dabo Fiase shekararta 54 a duniya, kuma tana yin takara ne a jam’iyyar ZLP.
Aondona ta taɓa zama ƴar majalisar jaha, kuma ta yi alƙawarin idan ta zama gwamna za ta kasance “sarauniyar aiki”
Borno Abubakar Fatima
Fatima tana da shekara 36 da haihuwa kuma tana takara ne a jam’iyyar ADC.
Cross RiverIbiang Marikana Stanley
Ibiang Marikana Stanley shekararta 41, tana takara a jam’iyyar ADP.
DeltaOnokiti Helen Agboola
Helen Agboola na da shekara 56 kuma a jam’iyyar Accord take takara.
Cosmas Annabel
Shekarar Cosmas Annabel 35 a duniya tana takara a jam’iyyar APP.
Yar kasuwa ce wadda ke da Diploma a jami’ar Ibadan kan abin da ya shafi alaƙar masana’antu da kuma yadda ake gudanarwa.
Ebonyi Igwe Chinenye Judith
Igwe Chineye Judith tana da shekara 37 a duniya, kuma a jam’iyyar APM take takararta.
Enugu Nweze Pearl Ogochukwu
Nweze Pearl Ogochukwu na da shekara 42 a duniya tana takara ne a jam’iyyar SDP.
Karatunta bai yi nisa ba ta tsaya ne iya makarantar sakandire
Jigawa Umar Binta Yahaya
Umar Binta Yahaya tana da shekara 42 tana takararta a AA.
‘Yar kasuwa ce da take gudanar da kasuwancinta ƙarƙashin kamfanin Yahaya Academy yayin da take da diploma kan harkar gudanarwa a kwalejin kimiyya da fasaha a Jigawa.
KanoYakubu Furera Ahmad
Furera Ahmed shekarunta 40 da haihuwa, yar jam’iyyar Boot ce inda take takara a ciki.
Mahmud Aishatu
Mahmud Aishatu Ahmed ta kai shekaru 53 kuma tana takara ne a NPM.
A jami’ar Bayero ta yi digirinta na farko kuma a nan ta yi na biyu inda daga nan kuma ta fara aiki tare da UBA, da ma’aikatar cikin gida da dai sauransu.
KwaraJaiyeola Motunrayo Deborah
Motunrayo Deborah na da shekara 41 tana takarar gwamna ne a jam’iyyar APM.
LagosKupoliyi Funmilayo
Kupoliyi Funmilayo yar shekara 31 na takarar gwamna ne a jam’iyyar APM ita ma.
Yar kasuwa ce da ta kammala karatunta a kwalejin kimiyya da fasaha ta Ogun inda ta karanta harkokin kasuwanci.
Adeyemi Abiola Roseline
Adeyemi Abiola Roseline, matashiya ce mai shekara 33 kuma ta fito takara ne a jam’iyyar APP.
Wata ‘yar kasuwa ta daban da ta yi digirinta na farko da na biyu a jami’ar Imo.
NasarawaTsakpa Patricia Danlami
Tsakpa Patricia Danlami tana da shekara 59 a ADP take takara.
Ta yi digirinta na farko a jami’ar Jos, ta kuma yi digirinta na biyu kuma a jami’ar karatu daga gida NOUN.
NigerAbdullahi-Iya Khadijah
Abdullahi-Iya Khadijah, yar shekara 48 ce a duniya, kuma tana takarar gwamna ne a jam’iyyar APGA.
Lauya ce kuma tana da ƙwarewa wajen yaƙi da cin zarafin mata, ita ce kuma shugaban ƙungiyar Women Community a nahiyar Afrika kuma ita ce shugabar mujallar S.I da dai sauransu.
Oyo Euba Aduragbemi
Shekarar Euba Aduragbem 37 tana takararta ne a jam’iyyar YPP.
Tana harkokin kasuwanci da kwalliya ne, ta kammala karatunta a jami’ar Lead da kuma kwalejin kwalliya ta Landan.
RiversItubo Beatrice
Itubo Beatrice tana da shekara 59 ita kaɗai ce mace ‘yar takara a jam’iyyar Labour.
Za ta yi takarar gwamna bayan aiki da ta yi a ƙungiyar ‘yan ƙwadago reshen jihar Rivers, kuma ita ce shugabar hukumar lafiya a matakin farko.
ZamfaraHadiza Bala Usman
Hadiza Bala Usman tana da shekara 35 tana takara ne a jam’iyyar ZLP.
Ta yi aiki a matsayin tsohuwar shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, kuma tsohuwar shugaban ma’aikatar gwamnatin Kaduna.
Kuma tana cikin manyan masu gangamin dawo da matan da aka sace na Chibok.