You are here: HomeAfricaBBC2022 09 20Article 1627205

BBC Hausa of Tuesday, 20 September 2022

    

Source: BBC

Matar da ke fargabar danta zai mutu bayan ta rasa gidanta sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan

Noor Zadi da jaririnta mai suna Sa'eedd Ahmad Noor Zadi da jaririnta mai suna Sa'eedd Ahmad

Daga Rajini Vaidyanathan BBC News, Sindh

"Ba zan iya zuba ido ina ganin jaririna na shan wuya ba", in ji Noor Zadi, a lokacin da take rungume da jaririnta mai suna Sa'eedd Ahmad, dan watanni 10.

Makonni kadan bayan ta rasa muhallinta sakamakon ambaliyar ruwa da ta fada wa Pakistan, a yanzu Noor na cikin tashin hankali saboda danta.

"Mu talakawa ne, ba mu da komai, mun damu da halin da yake ciki," in ji ta.

Yayin da likita ya soka masa allurar karin ruwa a jijiyar hannunsa, sai ya canllara kuka saboda azaba.

Saeed na bukatar a yi masa karin jini cikin gaggawa, saboda mummunan zazzabin cizon sauro da ya kama shi.

Iyalan Noor na daga cikin dubbai da ambaliyar ruwan Pakistan ta shafa, kuma suke bukatar magani.

Jami'an lafiya a yankin Sindh, da lamarin ya fi kamari, sun ce an samu karuwar masu kamuwa da zazzabin cizon sauro da amai da gudawa a dan tsakanin nan, saboda iyalai na zaune a wurare marasa tsafta, kuma a gamutse da juna.

Ba Sa'eed ne kadai ba jaririn da jami'an lafiya ke kula da shi a wani asibitin gaggawa da aka kafa a gundumar Thatta.
Zaune a can gefe cikin damuwa, wata uwa ce ta zuba tagumi, tana kallon jaririnta da ake yi wa karin jini.

Kusan duk marasa lafiyar da ke dakin yara kanana ne, kuma kusan dukkansu suna fama da cuta iri daya - amai da gudawa da zazzabin cizon sauro, kamar yadda Dr Ashfaque Ahmed, ya shaida min a wannan cibiyar lafiyar.

Lokacin da yake zagayawa da mu cikin dakin, Dr Ahmad ya gaya min cewa asibitin na fama da karancin kayan aiki da maganin zazzabin cizon sauro.

Ghulum Mustapha ya shigo dakin, sabe da jikar shi mai shekara biyu a kafada.

"Ruwa ya shafe gidana baki daya, na kaita wajen likitan da ke sansanin da muke zaune, amma babu abinda ya sauya don haka na garzayo nan", in ji Mustapha.

Can kusurwar dakin, wata matashiya, ce mai suna Shaista ce ta zubawa kasan dakin ido, ciki gare ta na watanni bakwai, kuma ita ma tana daga cikin wadanda ambaliyar ta yi wa mummunar barna.

Ba ta da cikakkiyar lafiya kuma an tura ta babban asibiti mai nisa daga inda ta ke, kamar yadda Dr Ahmad ya shaida min.

Babu abin da muke gani sai yadda marasa lafiya ke tururuwa zuwa nan.

Ba kowa ne ke samun damar zuwa asibiti a wannan lokacin ba. Mun isa wani sansani a yankin Damdama, nisan tafiyar rabin awa daga cibiyar lafiyar farko da muka ziyarta.

Wurin cike ya ke da dubun-dubatar yan gidun hijira. Bayan tsallake ruwan kogi, mun ga tarin gidajen da aka yi su da tantuna da duk abinda ya samu kama daga tanti domin rufewa, ga su nan masu tarin yawa.

Icce ko sanda mai kauri, da aka daurawa tsummokara ko kyallaye shi ya zanya wurin babu kyan gani, babu isasshiyar hanyar da iska mai tsafta za ta shiga, ga kuma tsananin zafin da ake yi.

Yawan wadanda suke zaune a wurin matasan iyalai ne, da muka fara tunkarar inda suje sai suka rugo su na tambayar ko mu likitoci ne.

Wata mace dauke da danta a kafada, tafe yana fama da zazzabi tsawon kwanaki hudu, ba ta da kudin kai shi asibiti.

Cikin wani tanti muka gano Rashida tare da 'ya'yanta 7, hudu daga ciki ba su da lafiya. Ita kan ta juna biyu gare ta na watanni 8, kuma ba ta da kudin da za ta kai kan ta ko yaran asibiti.

"Suna fama da zazzabi da amai da gudawa, sauraye sun cije su. Yarana su na kukan rashin madara," in ji Rashida.

Ta ce bata samun tallafin abinci ko tanti daga hukumomin Pakistan ba. Yawancin mazauna wurin sun yi kukan rashin taimako.

Wani babban jami'in gwamnati a Thatta mai suna Dr Ghazanfar Qadri ya amince ana fama da karancin tantuna, amma an kai agajin abinci yadda ya dace.

"Watakil ba za a rasa wadabda ba su samu taimakon ba, amma a gani na an yi abin da ya dace a wannan yankin," in ji shi.

Ya yin da Rashida ke fama da kan ta, da jiran lokacin haihuwa,ta san samu sassauci da ta samu labarin tallafi na tafe.

Sai dai hukumomi sun ce za a dauki watanni, kafin ambaliyar ta janye.

Yayin da muke tsaye a gefe guda, muna kallon daya tsallaken kogi, Rashida ta nuna min inda gidansu yake kafin ambaliyar.

Ta kara da cewa: "Ambaliyar ta shafe gidanmu baki daya, a yanzu ba mu da komai."

Read full article