You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837736

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

    

Source: BBC

'Mazauna Birnin Gwari na cikin taskun hare-haren 'yan Fashin daji'

Hoton alama Hoton alama

Ga dukkan alamu 'yan fashin daji masu garkuwa da mutane sun dawo da ayyukansu a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suke cin karensu babu babbaka.

Wasu jama'ar yankin sun bayyanawa BBC cewa kwanaki tara 'yan fashi suka kwashe suna tare hanya har suka yi awon gaba da mutane, al'amarin da ya tilastawa direbobi canza hanya a yanzu.

A baya hankulan mazauna wannan yanki ya kwanta amma a yanzu yan fashin daji sun hana jama sakat kamar yadda wani mutum ya bayyana wa BBC.

Mutumin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida cewa babu ranar da masu garkuwa da mutane ba za su fito su dauki mutane a hanyar Birnin Gwari ba zuwa Kaduna.

Ya ce: "kasancewar akwai shingen jami'an tsaro a hanyar Kaduna zuwa Buruku da Buruku zuwa Udawa da kuma Udawa zuwa Kuriga, shingen jami'an tsaron na da tazara a tsakaninsu wannan ce ta ba 'yan fashin dajin damar fitowa su kai wa matafiya farmaki''.

'Yan fashin dajin sun yi garkuwa da aƙalla mutane 44 a kwanaki tara da suka shafe a jere suna fitowa.

Wani direba ya koka game da yadda masu garkuwa da mutanen suka tilasta musu canza hanya.

''Direbobinmu sun kauracewa hanyar gaba-ɗaya saboda bin hanyar ya zama tashin hankali.

A ranar Asabar da na bi hanyar ɓarayin sun tare hanyar har sun kwashi kusan mutane 20''.

Shi ma wan direban daukar fasinja ma'abocin bin hanyar ta Birnin Gwari ya ce a baya kusan kullum suna bin hanyar amma a yanzu al'amuran tsaro sun tabarbare.

"Yanzu kullum muna cikin fargaba saboda masu garkuwa da mutane sun rufe hanyarmu, da kyar mu ka tsallake rijiya da baya cikin Ikon Allah, a cewarsa.

Wane mataki rundunar 'yan sandan Kaduna ke dauka?

Duk da cewa Rundunar 'yan sanda ta Kaduna ba ta fito filli ta amsa karuwar hare-hare a wannan yanki na Birnin Gwari ba, ta nuna cewa tana iya kokarinta wajen shawo kan matsalolin tsaron yankin

Mukaddashin kakakin rundunar 'yan sandan, ASP Mansur Hassan ya shaidawa BBC cewa a yanzu haka kusan duk cikin dazukan nan na Neja da Kaduna da Katsina gurare ana yakar masu garkuwa da mutane.

Sai dai kuma ya ce a wasu lokutan tsoro ya na sanya mutane su bayar da adadin da ba sahihi ba.

Gwamnan Jihar Kaduna ya gana da duk jami'an tsaro don tattauna sabbin matakan daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane.

Yankin Birnin Gwari dai guda ne daga cikin yankunan Jihar Kaduna da suke fama da 'yan bindiga bayan jihohin Katsina da kuma Zamfara.

Read full article