You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853951

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

    

Source: BBC

Me Uba Sani da Isa Ashiru ke cewa kan hukuncin kotun zaɓen Kaduna?

Isa Ashiru da Gwamnan Kaduna Uba Sani Isa Ashiru da Gwamnan Kaduna Uba Sani

A ranar Alhamis, kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan jihar Kaduna ta yanke hukunci kan ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru ya yi.

Sai dai kowane ɓangare na iƙirarin samun nasara.

Wakilan ɓangarorin biyu sun halarci zaman kotu a ranar Alhamis, sai dai alkalan ba su bayyana ba, inda suka yanke hukuncin ta amfani da manhajar Zoom.

Babu dai wani cikakken bayani kan dalilin karanta hukuncin ta manhajar Zoom, sai dai ana ganin lamarin ba zai rasa nasaba da batu na tsaro ba.

Kusan dukkanin ɓangarorin biyu na iƙirarin nasara, sai dai yayin da Uba Sani ke cewa shi ne ya samu nasara a zo a yi aiki tare, Isa Ashiru na cewa duk da nasarar da ya samu a kotun yana tattaunawa da lauyoyinsa don zuwa mataki na gaba.

Mataki na gaba 'Ya rage wa Isa Ashiru' - Uba Sani

Da yake magana, gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce hukuncin kotun ya ƙara tabbatar da nasarar da ya samu ne a lokacin zaɓe, saboda a cewar sa zaɓe ne da aka gudanar cikin gaskiya da adalci.

"Mu da Allah ya bai wa nasara, da takwarana na PDP da bai yi nasara ba, dukkanmu mu sani cewa Allah ne ke ba da mulki. Ina son in jaddada wa mutanen Kaduna cewa za mu yi wa kowa adalci," in ji Uba Sani.

"Zuwa kotu da Isa Ashiru ya yi abu ne mai kyau, saboda a kotu ne za ka je ka nemi hakkinka."

Ya ce kafofin sada zumunta ne da kuma wasu mutane suka riƙa yaɗawa cewa Isa Ashiru ne ya yi nasara a kotun wanda kuma ya ce farfaganda ce kawai.

"Mu ba ma bin maganar jita-jita saboda kowa ya ji hukuncin da alkalai suka yanke. Ya rage ga Isa Ashiru na ya yi tawakalli ga Allah," in ji shi.

Gwamna Sani ya ce ba su da wata fargaba ko da ɗan takarar jam'iyyar ta PDP zai ɗaukaka ƙara a gaba.

Sanata Sani ya ƙara da cewa abin da suka mayar da hankali a yanzu shi ne ci gaba da cika alkawura da gwamnatinsa ta yi wa ƴan jihar Kaduna.

Shure-shure ba ya hana mutuwa - Isa Ashiru

Sai dai shi ma a martaninsa, Hon Isa Ashiru, ɗan takarar gwamnan jihar ta Kaduna karkashin jam'iyyar PDP, ya ce shure-shure ba ya hana mutuwa kuma nasara ta su ce.

Ya ce "Kotu ta ce Hukumar zaɓe ba ta yi daidai ba wajen bai wa Uba Sani takardar cin zaɓe."

"Biyu daga cikin alƙalan sun ce a janye satifiket ɗin sai an je an sake zaɓuka a wasu rumfuna na jihar Kaduna.

Ya ƙara da cewa "Mun bai wa lauyoyin mu su duba hukuncin da aka gabatar don sanin mataki na gaba da za mu ɗauka."

Ashiru ya ce ba kan raɗin kansa yake kalublantar sakamakon zaɓen ba, illa don al'ummar jihar Kaduna.

Ya ce za su duba hukuncin kotun idan bai yi musu ba za su dangana gaba saboda wannan matakin farko ne ake.

"Wannan batutuwan zaɓe da muke zuwa kotu, zan tabbatar muku ba don kaina nake yi ba, magana ce ta al'ummar jihar Kaduna."

Me kotu ta ce?

Hukuncin kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Victor Oviawe, ya ce masu ƙorafin sun gaza karɓar sanarwar kafin fara shari'a (pre-hearing notice) a cikin mako ɗaya, kamar yadda sashe na 18 na kundin zaɓe ya tanada.

Haka zalika, kotun ta tabbatar da da'awar ɓangaren APC, Sanata Uba Sani cewa shaidun da Isa Ashiru ya gabatar, ba su da tushe.

Kotun ta kuma soki da'awar lauyoyin Uba Sani na cewa masu ƙorafi sun shigar da ƙara, bayan lokaci ya wuce, don haka ta yi watsi da buƙatar da suka nema.

Abin da lauyoyi suka ce

Lauyan APC

Lauyan jam'iyyar APC, Sanusi Musa mai lambar SAN ya shaida wa BBC cewa kotun zaɓen ta kori ƙarar da ɗan takarar PDP ya shigar.

Ya ce kotun yi watsi da buƙatar PDP ta neman a soke zaɓen, bisa hujjar cewa an yi maguɗi, amma dai kotun ta ce masu ƙorafin, ba su iya tabbatar da iƙirarin da suka yi ba.

Haka zalika, Sanusi Musa ya ce kotun ta kuma kori buƙatar ɗan takarar PDP na cewa ta tabbatar da Isah Ashiru, a matsayin wanda ya lashe zabe.

Ya ce lauyoyin APC sun soki ƙorafin PDP tun da farko na cewa, ba su shigar da ƙarar a kan lokaci ba.

A cewarsa, game da wuraren da aka soke zaɓe, kawunan alƙalan sun rabu biyu.

"Mutum biyu suka ce an soke zaɓe a akwatuna 22, kuma yawan ƙuri'un da suke wurin ya kai 16,000. Amma shugaban kotun ya ce inda aka soke zaɓen, yawan akwatunan ba su kai 22 ba, kuma yawan ƙuri'u 7,000 ne, saboda haka bai dace a ce za a taɓa sakamakon zaɓen ba."

A cewar lauyan APC, muhimmin abu dai daga ƙarshe, an kori ƙarar yanzu. "Babu ƙarar a kotu, kuma shi Sanata Uba Sani, shi ne gwamnan Kaduna."

BBC ta tambaye shi game da umarnin kotu na cewa a sake zaɓe a wasu tashoshin zaɓe. Sai Sanusi Musa ya ce "wannan ta faɗa ne. Ai ta riga ta kori ƙarar daga farko".

Lauyan PDP

Sai dai, Barista Baba Lawal Aliyu, lauyan Isa Ashiru ya shaida wa wakilin BBC da ya halarci zaman kotun cewa hukuncin da kotu ta gabatar, shi ne a je a sake zaɓe a ƙananan hukumomi guda huɗu cikin wasu mazaɓu kusan 14.

"A kotun, alƙalai ne guda uku, alƙalai biyu su ne masu rinjaye, kuma suka ce a je a sake zaɓe a ƙananan hukumomi guda hudu, shi kuma alƙali ɗaya ya ce ya tabbatar da Gwamna (Uba Sani).

Barista Baba Aminu ya ce hukunci iri biyu ne.

"Akwai hukuncin da kotun ta yi cewa sun watsar da ƙarar, saboda rashin shigar da ita a kan lokaci. Sannan kuma akwai hukuncin da ke cewa a sake zaɓe."

Ya jaddada cewa kotun, hukunci guda biyu ta bayar kuma za su ɗaukaka ƙara a kan ɓangarorin da ba su amince da su ba.

Tun farko Isah Ashiru na jam’iyyar PDP ne ya shigar da ƙarar, inda ya yi zargin tafka maguɗi a zaɓensu na watan Maris.

Sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, ta fitar a watan Maris, ya nuna cewa Sanata Uba Sani na APC, ya samu ƙuri’a 730,002.

Yayin da Isa Ashiru na PDP ya tashi da ƙuri’a 719,194.

Read full article