BBC Hausa of Tuesday, 17 January 2023
Source: BBC
Babban bankin Najeriya ya sanar da dawowar gwamnan bankin Godwin Emefiele daga hutu a ranar Litinin bayan wasu jita-jita da aka yaɗa sun ce yana ta gudu domin kada hukumar DSS ta kama shi.
A wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar, daraktan watsa labarai na bankin Osita Nwanisobi ya bayyana cewa "gwamnan ya dawo domin ci gaba da aiki da ƙarfinsa kafin taron farko kwamitin tsare-tsare na bankin da za a gudanar a ranakun 23 da 24 ga watan Janairun 2023."
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a shirye Mista Emefiele yake ya ci gaba da bin dokokin ƙasar da kuma umarnin Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari.
A ɗayan ɓangaren kuma hukumar tsaro ta DSS ta fitar da sanarwa inda ta ce jami'anta ba su kai samame Babban Bankin Najeriya CBN ba haka kuma ba su kama shugaban bankin ba.
"Muna jan hankalin al'umma kan labarin ƙaryar da yake yawo kan cewa jami;anta sun kai samame DSS tare da kama gwamnan.
"Wannan labarin ƙarya ne," in ji mai magana da yawun DSS Peter Afunanya.
Ya aka yi lamarin ya kawo haka?
An fara samun rahotannin yunkurin kama Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya da 'yan sandan farin kaya ta DSS suke son yi ne a watan Disamban 2022.
Wannan ya biyo bayan watsi da bukatar kama Emefiele ne da wata babbar kotu a Abuja ta yi da DSS suke son yi.
Wani mutum ne mai suna Gambarawa ya shigar da ƙara a madadin DSS a ranar 7 ga watan Disamban 2022.
Hukumar tsaro ta DSS ɗin ta zargi gwamnan babban bankin da cewa yana taimaka wa ayyukan ta'addanci saboda ya aikata laifi da ya shafi tattalin arziki.
Mai shari'a John Terhemba wanda ya jagoranci zaman ne ya kori ƙarar da aka shigar.
Ya ce DSS ba su gabatar da ƙwararan hujjoji ba da za su nuna gwamnan na da hannu a taimaka wa ta'addanci da aikata laifuka da suka shafi tattalin arzikin ƙasa.
Ƙungiyoyi na ganin fitar da sabbin kuɗi ne suka jefa Emefiele cikin matsala
Tun bayan da babban bankin Najeriya ya sanar cewa za a fara amfani da wani sabon tsari wanda ya haifar da samar da sabbin takardun Naira, gwamnan CBN ke ta fuskantar matsin lamba.
Majalisar dattawa ta ki amincewa saboda damuwar da ta nuna kan sabon tsarin, hakan ya zo ne bayan da Ministar Kudi ta Najeriya, Zainab Ahmed ta ce ba ta da labarin sabuwar dokar.
Haka kuma, majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan domin ya amsa tambayoyi kan sabbin takardun Naira da za a fara amfani da su da kuma yadda za su shafi tattalin arziki.
Wasu lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama da mambobin jam’iyyun adawa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu sun fara zanga-zanga a kan tituna domin adawa da matsin lambar da Emefiele ke fuskanta.
Masu zanga-zangar karkashin hadakar kungiyar masu kare muraddun ƙasa ta CNID sun ce hukumar tsaro ta farin kayan, DSS ta shigar da karar ne don neman a binciki gwamnan kan zargin taimaka wa ta’addanci.
Hadakar ta yi kira ga Shugaba Buhari da Atoni janar na Najeriya, Abubakar Malami da su saka baki cikin lamarin.