BBC Hausa of Monday, 27 March 2023
Source: BBC
Isra'ila ta shiga wani hali na fuskantar gagarumar zanga-zanga da ba ta taɓa gani ba a tarihi, inda mutane ke adawa da tsarin da gwamnatin ƙasar ke son yi na sauya yadda ɓangaren shari'ar ƙasar ke aiki.
Ga takaitaccen bayani kan abin da ke faruwa a ƙasar a halin yazu.
Me yake faruwa a Isra'la?
Tun farkon wannan shekarar mutane suka fara haɗa manya-manyan zanga-zanga ta mako-mako domin nuna adawa da shirin gwamnati na kawo sauyi a wasu tsare-tsarenta.
Zanga-zangar ta yi ta yaɗuwa, inda dubban ɗaruruwan mutane suka mamaye titunan Tel Aviv - birnin kasuwancin ƙasar - da kuma da wasu birane da garuruwa a faɗin ƙasar.
Masu zanga-zanga sun yi kira da a soke shirin kawo sauyi da Firaminista Benjamin Natenyahu ke son yi, inda suka bukaci da ya sauka daga mulki. Ƴan adawarsa na siyasa su ne ke jagorantar zanga-zangar, koda yake tsananin adawa da sauye-sauyen ya kasance cikin ƴan siyasa.
Wasu sojoji ma da suka kasance ƙashin bayan dakarun Isra'ila - sun nuna adawarsu da sauyin ta hanyar ƙin zuwa aiki, inda hakan ya ƙara nuna fargabar da ake da ita na cewa yanayin tsaron ƙasar na cikin barazana.
Mene ne ya tunzura mutane?
Abokan adawar mista Netanyahu sun ce sauye-sauyen za su saɓa wa tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar ta hanyar gurgunta tsarin shari'a wanda a tarihi ke bibiya ko sanya ido kan yadda gwamnati ke amfani da ikonta.
Wannan ita ce adawa mafi karfi ga wata gwamnati da ke kan karagar mulki - ta masu tsatssaurar ra'ayi a tarihin Isra'ila - da kuma shi kansa Mista Netanyahu.
Masu suka sun ce sauye-sauyen za su kare mista Netanyahu, wanda a halin yanzu ake tuhumar sa da laifin cin hanci da rashawa - tuhume-tuhumen da ya musanta - da kuma taimaka wa gwamnati wajen zartar da dokoki ba tare da taka-tsan-tsan ba.
Wane irin sauyi ne ya janyo zanga-zangar?
Damuwar ita ce karfin gwamnati da kuma karfin kotuna na ganin sun tantance har ma da yin watsi da bukatun gwamnati. Gwamnatin - da wasu - sun ce sake fasalin ya wuce lokacinsa, koda yake tsare-tsaren sun wuce fiye da yadda mutane da yawa ke so.
Ƙarkashin tsare-tsaren gwamnati:
. Ƙarfin Kotun Koli na sake dubawa ko fitar da dokoki zai ragu, tare da mafi rinjaye na ɗaya daga cikin Knesset (majalisar dokoki) na iya soke hukuncin kotu.
. Gwamnati za ta yanke hukunci kan wanda zai zama alkali, ciki har da Kotun Koli, ta hanyar kara yawan wakilci a kwamitin da ya naɗa su.
. Ba za a buƙaci ministoci su yi biyayya ga shawarar masu taimaka musu ba na ɓangaren shari'a - wanda babban lauyan gwamnati ke jagoranta - wanda a halin yanzu doka ta bukaci da su yi.
An riga an zartar da wani sauyi guda ɗaya a matsayin doka - cire ikon da babban lauyan gwamnati ke da shi na ayyana shugaba mai ci a matsayin wanda bai cancanta ya yi jagoranci ba.
Shin gwamnati za ta janye batun sauyin da take son yi ne?
Mista Netanyahu ya nuna turjiya ya zuwa yanzu, yana zargin shugabannin masu zanga-zangar da yunkurin kifar da gwamnati.
Ƴan adawar dai sun yi watsi da shawarwarin da gwamnatin ƙasar ta gabatar na sauya wasu sassa na shirin, suna masu cewa suna son a dakatar da su gaba ɗaya kafin a shiga tattaunawa, yayin da gwamnatin ta yi watsi da matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka.
Gwamnati dai ta ce masu kaɗa kuri’a sun zaɓe ta ne bisa alkawarin yin garambawul a ɓangaren shari’a, inda ta ce yunkurin hana ta ya saɓa wa tsarin dimokraɗiyya.
Haka kuma ana ganin ɓangaren shari'a na da sassaucin ra'ayi sannan kuma tsarin naɗa sabbin alkalan ba shi da wakilci.
Sai dai matsin lamba kan gwamnati na ƙaruwa a kullu-yaumin kuma ministan tsaron ƙasar da mista Natenyahu ya naɗa, ya yi magana kan sake fasalin ɓangaren shari'a - lamarin da ya sa firaministan ya kore shi daga mukaminsa.