BBC Hausa of Wednesday, 19 July 2023
Source: BBC
Yau ne ɗaya ga watan Muharram, shekarar 1445 bayan hijira. Ita ce rana ta farko a kalandar Musulunci.
An fara amfani da watannin Musulunci ne bayan hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.
Wannan ne dalilin da ya sa ake rubuta ta 1445 A.H, ma'anar 'A' din na nufin bayan hijira, yayin da 'H' din ke nufin hijira.
Ba wani watan da za a ce ga iyakar kwanakin sa kamar yadda yake a shekarar Turawa, kasancewar ganin wata ne ke tantance kwanakin kowane wata.
Yawanci akan samu bambancin kwanaki 11 tsakanin shekarar Musulunci da ta Turawa, yayin da ta Musulunci ke da mafi arancin kwanaki.
Muslimai na murnar sabuwar shekarar ne saboda tunawa da hijirar da Annabi Muhammad (SAW), daga Makka zuwa Madina.
Hakan yana da mahimmanci a Musulunci saboda yana taimaka wa Musulunci wajen ƙara fahimtar asalin inda aka samo shekarar da kuma yadda Musulmai suka zama tsintsiya ɗaya.
Babu wani nau'in ibada da aka tanada a ranar ɗaya ga watan Muharram na kowace shekara, sai dai ana so Musulmi su riƙa tunawa da gwagwarmayar da Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa suka sha kafin Musulunci ya samu tsayuwa da ƙafafunsa.
Haka kuma ana shawartar Musulmi da su riƙa azumtar ranar ɗaya ga watan Muharram da kuma addu'o'i a kowace shekara.
Jerin watannin shekarar Musulunci