You are here: HomeAfricaBBC2023 05 13Article 1766537

BBC Hausa of Saturday, 13 May 2023

    

Source: BBC

Me ya sa shugabannin ƙasa ke son yi wa Majalisar Najeriya tuwona-maina?

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Kimanin mako biyu a rantsar da sabuwar gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a Najeriya, amma ƙura na ci gaba da turnuƙewa a fagen siyasar ƙasar game da shugabanci majalisa ta goma.

Jam’iyya mai mulki wato APC ta ce tana nan kan matsayinta na goyon bayan Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin a matsayin shugaban Majalisar Dattijai da mataimakinsa, da kuma Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin shugaban Majalisar Wakilai da mataimakinsa.

Sauran masu neman shugabancin a majalisun biyu, sun yi tattaki har shalkwatar APC a Abuja, inda suka gabatar da rashin yardarsu a kan matakin uwar jam’iyyar tasu.

A ranar Juma’a ma, mataimakin shugaban Majalisar Wakilai mai ci, Ahmed Idris Wase ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin sabuwar majalisar da za a buɗe nan gaba a watan gobe.

APC dai ta ce ta raba muƙaman ne don tabbatar da adalci da tsarin raba daidai a tsakanin shiyyoyi guda shida na Najeriya, sai dai masu adawa da matakin sun ce yin haka, rashin adalci ne tun da majalisa gashin kanta take ci, kuma jama’a take wakilta, ba jam’iyya ko wani shugaba ba.

Yayin da wasu ke kallon lamarin da cewa yunƙuri ne na shiga aikin majalisar, don ganin ta zama ‘yar amshin shata ga ɓangaren zartawa.

BBC da haɗin gwiwar Gidauniyar McArthur a baya-bayan nan ta gayyaci wasu masu ruwa da tsaki wani taro don tattaunawa a kan ko me ya sa shugabannin ƙasa a Najeriya ke son tabbatar da shugabancin majalisa?

Katsalandan

Wani babban ƙalubale da majalisun dokoki ke fama da shi a Najeriya in ji wani masanin kimiyyar siyasa, Mallam Kabiru Sufi, shi ne katsalandan.

A cewarsa, ko kasafin kuɗi ɓangaren zartarwa ya kai don a zartar da shi zuwa doka, to ba a sakarwa majalisa mara ta yi abin da ya dace.

Ya ce lokaci zuwa lokaci, ɓangaren zartarwa yana ƙoƙarin ganin ya shiga cikin aikinsu, ko kuma ya tursasa musu, su yi wani abu da bai kamata ba.

Mallam Sufi ya ce hakan kuma yana kawo tarnaƙi a ayyukan majalisa, ta yadda matakin ke zagon ƙasa ga tsarin rabon iko daidai tsakanin ɓangarorin gwamnati uku.

Shi ma, zaɓaɓɓen sanata kuma tsohon ɗan majalisar wakilai, Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce matuƙar 'yan majalisa za su yi aikinsu na yin doka da bibiyar ayyuka yadda ya kamata, to ɓangaren zartarwa ba zai miƙe ƙafa yadda yake so ba.

Ya yi zargin cewa ɓangaren zartarwa musamman a ƙasashe masu tasowa na son ganin ya yi 'cinye duk' wato ya tattare ikon komai a ƙarƙashinsa.

Shi kuwa wani ɗan fafutuka daga ƙungiyar wayar da kai kan ayyukan 'yan majalisa (CISLAC) Auwal Musa Rafsanjani, cewa ya yi abu ne mai muhimmanci a samu haɗin kai tsakanin majalisar dokoki da ɓangaren zartarwa.

Amma ba haɗin kan da zai hana majalisa ta yi aikinta na kare tsarin mulki da muradan al'ummar ƙasa ba, in ji shi.

A cewarsa, lamarin zai fi muni, idan majalisa ta kasa aikinta a lokacin da ake ganin ɓangaren zartarwa yana wuce gona da iri.

Kawu Sumaila dai ya yi iƙirarin cewa, akwai rashin dacewa a ce "wani mutum a ɓangaren zartarwa ne zai naɗa shugabanni a majalisun da ke wakiltar muradan ‘yan ƙasa".

“Sunansu Majalisun ƙasa, masu wakilcin jama'ar da suka zaɓo su don kare muradansu,” in ji zaɓaɓɓen sanatan.

Tasirin gwamnoni

Wasu mutane da yawa a ƙasar na ra’ayin cewa gagarumin ikon da gwamnoni ke da shi a harkokin mulki da na siyasa, na cikin ƙalubalen dimokraɗiyya a Najeriya.

Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce maganar gwamnoni da cewa jagoranci na jam’iyya a hannunsu yake, babban tarnaƙi ne dimokraɗiyyar ƙasar.

“Matuƙar gwamna ne zai naɗa shugaban ƙasa. Shi zai naɗa shugaban majalisar dattijai. Shi zai ba da mataimakin shugaban ƙasa. Da shugabannin jam’iyya. Ya naɗa kansila. Ya naɗa ɗan majalisar tarayya da kowa da kowa. Sai abin da yake so, to ba mutane za a wakilta ba, gwamna za a wakilta”, in ji shi.

Ghali Umar Na’abba ya ce ‘yan majalisa da yawa ba su cancanta ba, don haka idan sun zo majalisa, aikin gwamna suke yi ba na jama’a ba. “Duk abin da gwamna ba ya so, ba za ka ga ana tattauna shi a majalisa ba”.

Auwal Musa Rafsanjani ya ce akwai buƙatar yi wa tsarin mulkin Najeriya garambawul don rage ɗumbin ikon gwamnoni, matuƙar ana so abubuwa su ci gaba ta fuskar mulkin dimokraɗiyya ƙasar.

Ikon gwamnoni a Najeriya ya yi yawa. A cewarsa: “Hatta shugaban ƙasa, tsoronsu yake ji. Su ne za su kawo masa ministoci, su ne za su kawo masa mutanen da zai naɗa shugabannin hukumomi da jakadu.

Kawu Sumaila ya ce dole ne tun daga matakin zaɓe, a riƙa ɗauko ‘yan majalisar da za su yi al’umma alƙawari maimakon tsarin da ake kai wanda gwamna yake nuna mutanen da za su kasance 'yan majalisa.

Tasirin kuɗi

Wasu kuma na ganin tasirin kuɗi na cikin manyan matsalolin da ke janyo nakasu ga tsarin dimokraɗiyya ciki har da batun tafiyar da majalisa a Najeriya.

Wani tsohon ɗan majalisar jiha a Kano, Hon Rabi'u Saleh Gwarzo ya ce rashin 'yancin cin gashin kai musamman a matakin jiha na da alaƙa da zama 'yan amshin-shata a ƙasar.

A cewarsa duk lokacin da aka ce wani abu ya samu majalisa, amma sai ta ɗauki ƙoƙo ta tafi ga gwamnati don neman kuɗin kamar sayen ababen hawa da shirya tarukan ƙarawa juna sani, wannan ba ƙaramar matsala ba ce.

Ya ce irin wannan yanayi na ɗaukar ƙoƙo don samun biyan buƙatun wasu haƙƙoƙi daga gwamnati, yana ba da yanayi da gwamnatin ke zuwa da wasu abubuwa da take so a yi mata, ko da ana ganin ba sa kan doka.

Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce dole ne sai majalisa ta yi nazari da kanta kan harkokin kuɗi tsakaninta da ɓangaren zartarwa.

"Sai ta tsarkake kanta wajen mu'amalarta da ɓangaren zartarwa ta fuskar hada-hadar kuɗi. Mu'amalarta ta cikin gida game da kuɗi, a fassara kowanne kuɗi da ya shigo, a fayyace abin da aka ce a yi da shi, da kuma yadda za a yi da shi".

Ya ce dukkan wanda zai yi gyara, sai ya fara duban kansa ya yi gyara.

A cewarsa, kamata ya yi 'yan ƙasar su mayar da hankali wajen sa ido kan majalisun ƙasar don ganin kuɗaɗen da ake ware musu, ana amfani da su wajen inganta tsarin ayyukan majalisa da kuma bibiyar harkokin ɓangaren zartarwa.

Kabiru Sufi ya ce aikin majalisa, harka ce mai buƙatar kashe ɗumbin kuɗaɗe, hatta aikinsu na bibiyar ayyukan ɓangaren zartarwa.

Ya ce kuma duk lokacin da aka samu canji, aka zaɓi sabbin ‘yan majalisa akwai buƙatar a horas da su.

Ƙarancin wayewar siyasa

Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ya ce matuƙar 'yan majalisa ba su san ƙarfinsu ba, kuma ba su san dokokinsu ba, kuma ba su da jajircewa to zai yi wahala su yi abin da ya kamata.

Ita ma, Hajiya Saudatu Mahadi daga ƙungiyar Wrapa mai fafutukar kare haƙƙoƙin mata a Najeriya ta ce a cikin ƙalubalen da 'yan majalisa a Najeriya suke fuskanta akwai rashin fahimtar haƙƙin da ke kansu, da kuma ƙarancin ilmi.

Ta ce 'yan majalisa da yawa a matakin tarayya suna zuwa ne, ba tare da sun san nauyin da ke kansu ba.

Hajiya Saudatu Mahadi ta ƙara da cewa wata babbar matsala a Najeriya ita ce yadda dole sai ɗan takara ya tsaya a ƙarƙashin inuwar wata jam'iyya kafin ya a iya zaɓarsa zuwa majalisa.

"A ƙasashen da suka ci gaba, ana samun daga ta yadda mutane ingantattu kuma masu kishin ƙasa, da za su tsaya takara a matsayin indifenda, har su ci zaɓe.

Zaɓaɓɓen sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya yi iƙirarin cewa tun da Najeriya ta koma kan turbar dimokraɗiyya a 1999, ƙasar ba ta yi majalisa kamar wadda za a buɗe a watan Yuni ba.

"Bambancinsu shi ne a majalisar wakilai cikin su 360, 'yan majalisar adawa waɗanda ba a jam'iyyar gwamnati suke ba, sun fi yawa".

Ya ce idan suka tsaya suka dage, to sai abin da suke so ne, zai faru a majalisar, ba yadda gwamnati take so a yi ba, tun daga kan shugabanci.

Haka zalika, a Majalisar Dattijai ma, in ji jam'iyya mai mulki ba ta da rinjayen biyu cikin uku na 'yan majalisa 109, lamarin da zai iya ƙalubale ga dokoki da manufofin gwamnati a zauren.

A cewarsa, ɓangaren 'yan adawa suna adadin kujera 50 idan sun dunƙule, abin da ka iya ba su wata dama ta musamman, wadda za ta tabbatar da ganin an dama da mutanensu.

Sabon sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu, ya ce amma ba lallai ne hakan ta tabbata ba, matuƙar mutanen da ake wakilta, ba za su riƙa bibiya suna tambayar wakilansu game da amanar da suka damƙa musu ba

Read full article