BBC Hausa of Monday, 27 March 2023
Source: BBC
Ibadar azumi tana buƙatar mutum ya ƙauracewa cin abinci da sha da kuma kusantar iyali daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.
Manufar ita ce jiki ya samu wani sauyi wanda bai saba ji ba, domin haka ne Ubangiji ya ce shi da kansa ke biyan lada ga mai azumi.
Sai dai a kan fuskanci matsaloli da dama a yayin azumin musammam ga sabbin aure ko kuma mutanen da suke ɓata-gari, wani lokacin kuma tsautsayi ya gifta ko da a kan waɗanda suka shafe shekaru ne da aure, a samu kuskure ta fuskar mu'amalar iyali.
Menene hukuncin wanda ya kusanci iyalinsa cikin azumi?
Menene hukuncin wanda ya yi wasa da matarsa har maziyi ya fita a cikin azumi da rana tsaka da gangan ko da sani?
BBC ta tattauna da Malam Halliru Abdullahi Maraya da ke birnin Kaduna, kuma ya yi bayani cewa wannan abu ba ƙaramin laifi ba ne a shari'ance.
"Idan mutum ya kusanci matarsa da rana cikin azumi, sai ya rama azumin sannan kuma ya yi kaffara ta azumin wata biyu a jere, sannan kuma a rama wanda aka ɓata.
"Amma idan akwai larura ta rashin lafiya da ba za ta iya bari ya yi azumi mai yawa haka ba a jere, ko wadda ba za a iya azumi ba idan ana fama da ita, ko kuma za ta ƙaru idan ana azumi to sai a hakura da yi, a ciyar da miskinai.
"Kullum sai an ciyar da miskini guda a madadin azumi guda," in ji Malam Halliru Maraya.
Idan azumi biyu ne haka zai yi azumi 120 a jere sannan kuma ya rama biyun da ya ɓata.
'Idan maziyyi ne ya fita garin wasa, akwai maganganun malamai kashi biyu'
Ba ƙaramin bala'i ba ne a ce mutum ya karya azuminsa ta kowacce hanya da Ramadana, dole mutum ya kiyaye, ya san Ubangiji zai iya hukunta shi kan haka.
Abin da ya fi muni shi ne karya azumi ta hanyar kusantar mace a tsakiyar azumi da rana.
"Idan maziyyi ne ya fita ko kuma dai abin da ya fita ba maniyyi ba ne, shi wannan babu kaffara a wurin mafi yawan malamai zai rama azumin wannan ranar ne.
"Ba zai ɗauki kansa cikin waɗanda suke azumi ba, kuma ba zai ci gaba da cin abinci ba saboda wannan matsala ta faru, domin kada ya keta alfarmar yinin.
"Idan kuma ya ci abinci to sai ya yi kaffara irin wadda aka bayyana ta watanni biyu a jere," in ji Malam.
"Wasu malamai sun ce idan ya fitar da maziyyin ne da gangan ta hanyar kallon matarsa har ya fita, ko ya rungume ta ko kuma ya sumbace ta, to sai ya yi kaffara.
"A wajen wasu malaman kuma ko da gangan ya yi iya azumin ranar zai rama kawai," in ji Malam.
An fi samun irin waɗannan kusakuran daga wajen sabbin aure da suke aure daf da azumi, wanda da za a kyale a yi hakurin makonni huɗun Ramadana da sai ya fi zama alkhairi ga kowa.