BBC Hausa of Monday, 8 May 2023
Source: BBC
Lionel Messi ya lashe kyautar fitatcen dan wasa, yayin da Argentina ta zama gwarzuwar tawaga ta shekara a bikin Laureus World Sports Awards.
Messi, kyaftin din Argentina ya ci kwallo bakwai da lashe kyautar kwallon zinare a gasar da kasarsa ta lashe kofin duniya a 2022 a Qatar a Disamba.
Shine na farko da ya lashe kyautar ta kashin kansa da kuma tare da tawaga a kaka daya.
Macen da ba kamarta a shekarar ita ce 'yar Jamaica, Shelly-Ann Fraser-Pryce, wadda ta lashe kyautar.
Ta lashe tseren mita 100 a gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya a Oregon a watan Yuli.
Hakan ya sa ta zama ta farko da ta lashe lambar yabo biyar a fannin guje-guje.
Fraser-Pryce mai shekara 36 ta fara lashe tseren mita 100 shekara 13 baya, kuma ita ce kan gaba a yawan lashe tseren fiye da kowa.
Dan wasan Manchester United da Denmark, Christian Eriksen yana cikin wadanda suka lashe kyautar, wanda ya farfado bayan faduwa a cikin fili tsaka da wasa a Euro 2020.
Shima Carlos Alcaraz yana cikin wadanda suka lashe kyautaR, bayan da matashi mai shekara 19 ya lashe US Open.
Jerin kyautukan da aka lashe:
Laureus World Sportsman of the Year award: Lionel Messi
Laureus World Sportswoman of the Year award: Shelly-Ann Fraser-Pryce
Laureus World Team of the Year award: Argentina men's football team
Laureus World Breakthrough of the Year award: Carlos Alcaraz
Laureus World Comeback of the Year award: Christian Eriksen
Laureus World Sportsperson of the Year with a Disability award: Catherine Debrunner
Laureus World Action Sportsperson of the Year award: Eileen Gu
Laureus Sport for Good award: TeamUp (A programme for children displaced by war by Barcelona and Poland striker Robert Lewandowski)