BBC Hausa of Tuesday, 17 January 2023
Source: BBC
Kociyan Argentina, Lionel Scaloni ya ce Lionel Messi ya sha gaban Diego Maradona a matakin fitatcen dan wasan tamaula a duniya.
''Idan an bani zabi a tsakaninsu Messi zan zaba, domin yana da wasu abubuwa na musamman a tare da shi.
Shi ne fitatcen dan kwallo a duniya, koda yake Maradona ma ya yi fice'' kamar yadda Scloni ya yi hira da gidan radiyon Cope a Argentina ranar Talata.
Mutane a Argentina sun fi kaunar Maradona fiye da Messi, sai dai watakila a samu sauyi nan gaba, bayan da dan wasan Paris St Germain ya ja ragama da Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar.
A watan jiya Argentina ta dauki kofin duniya na uku jumulla, kuma na farko tun bayan da Maradona ya lashe a 1986.
Scaloni ya ce ya samu damar magana da Messi a lokacin da aka nada shi kociyan Argentina a 2018, inda ya rarrashi dan wasan PSG bayan da kasar ta kasa kai bante a gasar kofin duniya a Rasha.
''Abin da muka fara yi shi ne kiran waya ta bidiyo da Messi, kuma ya ce an martaba shi, abin da na fara sanar da shi cewar muna bukatarsa.
Haka kuwa aka yi ya dawo wasa bayan wata takwas muna jiranshi daga nan muka samu nasarar da muke bukata.''
''Horar da Messi bai da wahala. Ba yadda za ka ci gyaransa, domin kwararre ne, wani lokaci za ka shawarce shi ya kara sa matsi - idan yana kan ganiya ba magana.''
Haka kuma Scaloni ya kare mai tsaron ragarsa, Emiliano Martinez kan yadda aka yi ta caccakarsa bisa dabi'a da ya nuna a lokacin da ya karbi kyautar golan da ba kamarsa a Qatar.
Haka kuma mai tsaron ragar ya rike 'yar tsana mai fuskar Kylian Mbappe a lokacin da Argentina ke zagaye birin a budaddiyar mota.''Akwai wasu halayae da ya nuna shi kansa zai yi dana sani, amma dai mai tsaron raga ne kwararre,'' in ji Scaloni.