You are here: HomeAfricaBBC2023 04 28Article 1757615

BBC Hausa of Friday, 28 April 2023

    

Source: BBC

Mike Pence ya ba da shaida kan binciken laifi da ake yi wa Trump

Tsohon mataimakin shugaban Amurka Mike Pence Tsohon mataimakin shugaban Amurka Mike Pence

Tsohon mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya bayar da shaida a yayin gudanar da binciken aikata laifin da ake zargin yunƙurin da Donald Trump ya yi na sauya sakamon zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2020 da ya sha kaye.

Mista Pence, mai shekaru 63, ya zauna na tsawon sa’oi bakwai a gaban wata tawagar alƙalai a birnin Washington DC, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa abokiyar hulɗar BBC, kafar yada labaran CBS ta Amurka ta ambata.

A farkon wannan shekarar ne aka aike masa da takardar sammaci zuwa kotun don ya bayar da shaidar.

An gudanar da tambayoyin da aka yi masa ne cikin sirri.

Bayyanarsa a ranar Alhamis na zuwa ne sa’oi kaɗan bayan da wata kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da wani yunƙurin da lauyoyin Mista Trump suka yi na dakatar da Mista Pence daga bayar da shaidar.

Lauyoyin Mista Pence sun kuma nemi ƙalubalantar sammacin wanda hakan bai samu nasara ba, inda suka ce rawar da ya taka a matsayinsa na shugaban majalisar datatwa lokacin da yake kan muƙaminsa na nufin yana da rigar kariya.

Shidar da aka nemi ya bayar da ake shafe watanni ana nema, wani gagarumin ci gaba ne a binciken da aka shafe shekaru biyu ana gudanarwa wanda lauya na musamman Jack Smith ke jagoranta, da kuma wani tsohon mai gabatar da ƙara kan aikata laifukan yaƙi da aka naɗa a matsayin babban lauyan gwamnati Merrick Garland.

Masu binciken sun ta tattara shaidu game dako shin Mista Trump da aminansa sun yi yunƙurin ƙalubalantar sakamakon zaben na shekarar 2020, wanda shugaba Joe Biden ya samu nasara.

Suna kuma gudanar da bincike musabbin hatsaniyar da ta faru a majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2021, lokacin da magoya bayan Mista Trump suka afka wa ginin a yunƙurinsu na hana bayar da takarsdar shaidar lashe zaɓen.

Mista Pence, kamar sauran mataimakan shugaban ƙasa, ya taɓa zama shugaban majalisar datattawa – wanda akasari mukami ne na je-ka-na-yi-ka, ka iya karkatar da batun bayar da takardar shaidar lashe zaben tare da jinkirta miƙa mulkin.

Mista Trump ya fito a bainar jama'a yana yin matsin lamba ga mataimakinsa da ya aikata hakan, kuma rashin yin hakan ya sa shi yiwa Mista Pence barazana.

Daga nan ne magoya bayan Trump suka rika rera taken ‘’a rataye Mike Pence’’ a yayin da suka abka cikin ginin majalisar dokokin ta cikin farfajiyar ginin a daidai lokacin da ‘yan siyasa da suka hada da Mista Pence, ke ciki.

Watch: Sabon faifen bidiyon da ke nuna Kakakin Majalisar Dokoki Pelosi lokacin farmakin na ranar 6 ga watan Janairu.

An daukar Mista Pence a matsayin wata muhimmyar shaida a cikin binciken, kana a yayain da babu wani tabbaci nan take kan abubuwan da ya shaida wa alkalaun, akwai yiwuwar masu gabatar da kara sun tambaye shi game da tattaunawar da suka yi da Mista Trump da ‘yan tawagarsa a cikin kwanaki da makonnin da suka kai ga yin hatsaniyar.

"Za mu bi doka, za kuma mu fadi gaskiya,’’ Mista Pence ya bayyana a wata hira da kafar yada labaran CBS a ranar Lahadi. ‘’ Labarin da nake bai wa mutanen Amurka a fadin kasar…shi zai kasance irin labarin da zan fada a wancan wuri.’’

Mista Pence ya fito fili ya yi bayani game da hatsaniyar da ta faru a ginin majalisar dokokin da kuma matsin lambar da ya fuskanta na ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen. ‘’ ShugabaTrump yi tafka kuskure. Ba ni da ‘yancin sauya sakamakon zaɓe,’’ ya ce a wani jawabi a cikin watan Fabrairu.

Abubuwan tunawarsa , Allah Ka Taimakeni, Mista Pence ya rubuta cewa Mista Trump ya yi yunƙurin matsa masa lamba, ana bayar da shaidar sakamakon zaɓen a safiyar faruwar hatsaniyar. ‘’ Za ka yi faɗuwar baƙar tasa!’’ shugaban ƙasar a wancan lokacin ya fito fili ya fad awa Mista Pence.

Ya kuma zargi Mista Trump da jefa rayuwar iyalansa da ma sauran jama’a da ke cikin ginin majalisar dokokin cikin hadari, yana mai cewa tarihi zai dora alhaki a kan sa.

An bayar da rahoton cewa Mista Pence na duba yiwuwar neman tsayawa takarar shugabancin ƙasa a shekarar 2024, wanda zai ƙalubalance tsohon ubangidansa kai tsaye a cikin wanda jam’iyar Republican za ta tsayar.

Mista Trump, wanda tuni ya ƙaddamar da aniyarsa ta sake dawowa fadar White House, na jihar New Hampshire a ranar Alhamis don gudanar da wani taron gangamu.

Lokacin da kafar yaɗa labaran NBC ta tambaye shi game da shaidar da Mista Pence ya bayar, ya mayar da martanin cewa: "Ban san me ya fada ba, amma ina da ƙarfin gwiwa sosai a kan shi."

Tsohon shugaban ƙasar na fuskantar sauran tuhume-tuhume, da suka haɗa da binciken da Mista Smith ke jagoranta kan wasu muhimman takardun masu cike da kura-kurai.

Akwai kuma wani bincike na daban a jihar Georgia kan zargin yunƙurin sauya sakamakon zaɓen shekarar 2020.

Read full article