You are here: HomeAfricaBBC2021 07 07Article 1303255

BBC Hausa of Wednesday, 7 July 2021

    

Source: BBC

Morata ya hana Sifaniya kai wa wasan karshe a Euro 2020

Morata na cikin yan Sifaniya da suka bata fenaritin kece raini Morata na cikin yan Sifaniya da suka bata fenaritin kece raini

Tawagar kwallon kafa ta Italiya ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2020, bayan da ta doke Sifaniya a bugun fenariti.

Tun farko kungiyoyin sun tashi 1-1 ne daga nan aka kara musu lokaci, duk da haka ba a samu gwani ba.

Italiya ce ta fara cin kwallo ta hannun Federico Chiesa, bayan da suka koma karawa ta biyu bayan hutu da suka yi.

Saura minti 10 a tashi daga wasan Sifaniya ta farke ta hannun Alvaro Morata.

Bayan da suka yi minti 120 ba a kara cin kwallo ba har da karin lokaci suna 1-1 ne aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga inda Italiya ta yi nasara da ci 4-2.

Wanda ya fara bararwa da Italiya fenariti shi ne Manuel Locatelli, wanda ya ci mata na gaba kuwa shine Andrea Belotti.

Sauran ukun da suka ci wa Italiya bugun daga kai sai mai tsaron raga sun hada da Leonardo Bonucci da Federico Bernardeschi da kuma Jorginho.

Dani Olmo ne ya fara buga wa Sifaniya fenaritin da kwallo ya yi saman raga, daga baya Gerard Moreno da kuma Thiago Alcantara suka zura a raga.

Sai dai Alvaro Morata, wanda ya farke wa Sifaniya kwallo, shi ne ya barar da fenaritin da kasar ta kasa kai wa karawar karshe.

Ranar Laraba za a buga daya wasan daf da karshe tsakanin Ingila da Denmark a Wembley.

Kuma duk wadda ta yi nasara a tsakaninsu za ta buga wasan karshe da Italiya ranar Lahadi a Wembley.

Read full article