You are here: HomeAfricaBBC2021 09 19Article 1360648

BBC Hausa of Sunday, 19 September 2021

    

Source: BBC

Muhamman abubuwa da suka faru a Najeriya a wannan makon

Shugaba Muhammadu Buhari da Femi Fani Kayode Shugaba Muhammadu Buhari da Femi Fani Kayode

Yayin da ake shirin shiga sabon mako, bari mu yi waiwaye kan wasu abubuwa masu muhimmanci da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata daga ranar Lahadi 12 ga watan Satumba zuwa Asabar 18 ga watan na Satumba.

Jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya ya yi aman wuta kan fararen hula

Wani jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya ya yi aman wuta a yankin ƙauyen Buhari da ke ƙaramar hukumar Yunusari a jihar Yobe da safiyar Laraba, 15 ga watan Satumba kuma ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.

Al'ummar garin sun shaida wa BBC cewa sun wayi gari ne da ganin jiragen yaƙi har uku suna shawagi a sararin samaniyar garin nasu.

Daga bisani ɗaya daga cikin jiragen ya yi aman wuta kan wani ɓangaren garin, kamar yadda wasu da suka shaida lamarin suka bayyana wa BBC.

Ɓullar wannan labarin ke da wuya, rundunar sojin Najeriya ta musanta aukuwar lamarin kuma ta ce ba hannunta a ciki.

Sai dai bayan kwana guda rundunar ta fitar da wata sanarwa inda ta ce bisa kuskure ne jirgin sojinta ya kai hari tare da kashe fararen hula a garin na Buhari da ke karamar hukumar Yunusari a jihar Yobe.

Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran rundunar sojin saman Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce jiragen sojin na shawagi ne yankin Kogin Kamadougou Yobe don tattara bayanan sirri kan ayyukan kungiyoyin Boko Hraam da ISWAP.

Shaidu sun ce harin jirgin saman na ranar Laraba ya yi sanadin kashe aƙalla mutum goma, baya ga gommai da suka jikkata cikinsu har da mata da ƙananan yara.

Rundunar ta ce a kafa wani kwamitin bincike kan abin da ya haddasa lamarin.

Jiri ya ɗebi Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa a taro

Ranar Alhamis 16 ga watan Satumba yayin gabatar da jawabi a wani taron Ranar Shaida a Najeriya, jiri ya ɗebi shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa.

Abdulrasheed Bawa na tsaka da yin jawabin nasa ne a fadar shugaban Najeriya sai ya dakata da yin magana kuma ya fara yamutsa fuska sannan ya sa tafin hannunsa ya riƙa shafa fuskar tasa.

Ya ce "ina tunanin zan dakata haka nan, na gode muku ƙwarai" sannan ya sauka daga kan dandamali ya nufi kujerarsa, inda wasu manyan jami'an gwamnati ciki har da ministan sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami suka tarbe shi kuma suka rirriƙe shi zuwa kujerar tasa.

Zamansa a kujerar ke da wuya, sai ɗaya daga cikin jami'an ya kwantar da shi a kan kujerar yayin da shi kuma Abdulrasheed Bawa ya ci gaba da dafe kansa.

An fitar da shugaban EFCC ɗin daga ɗakin da ake gudanar da taron kuma daga baya Farfesa Pantami ya sanar da cewa Abdulrasheed ya samu sauƙi.

Haka kuma, Hukumar EFCC ta fitar da sanarwa a ranar inda ta ce shugaban nata na cikin ƙoshin lafiya kuma ya koma bakin aikinsa.

FemiFani-Kayode ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

Tsohon ministan jiragen sama a Najeriya kuma babban mai sukar gwamnatin Shugaban Muhammadu Buhari, Femi Fani-Kayode ya sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC ranar Alhamis 16 ga watan Satumba.

Dama dai an daɗe ana raɗe raɗin cewa ministan zai koma APC daga jam'iyyar da ya jima yana kare wa faɗa musamman a shafukan sada zumunta wato PDP, kuma tsohon ministan ya sha musanta wannan jita-jita.

Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Gwamna Mai Mala Buni ne suka tarbe shi a fadar shugaban kasa.

Femi Fani-Kayode ya ce ya sauya sheƙar ne saboda yana ganin hakan ne mafi dacewa a dai-dai wannan lokacin kuma yana da burin taimaka wa Shugaba Buhari don ciyar da Najeriya gaba.

Lauyoyin Sheikh Abduljabbar sun janye daga wakiltarsa, asibitin ƙwaƙwalwa na Dawanau ya ce malamin lafiyarsa ƙalau

A ci gaba da zaman sauraren ƙarar malamin da ake yi, duka lauyoyin Sheikh Abduljabbar ba su halarci zaman kotun ba na ranar Alhamis 16 ga watan Satumba.

Wakilin BBC da ya halarci zaman kotun ya ce lauyan Abduljabbar ɗaya ne ya je kotun, wato Barista Haruna Magashi kuma take ya ce ya janye daga wakiltar malamin.

Ya kuma ce "Sauran lauyoyin su ma sun janye daga kare Abduljabbar shi ya sa dukkansu babu wanda ya halarci zaman kotun.

Haka kuma, asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa na Dawanau da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ya ce Abduljabbar Kabara ba shi da matsalar kwakwalwa.

Sai dai asibitin ya ce an taɓa kwantar da shi a asibitin tsawon kwana huɗu lokacin da ya taɓa yin rikici da ɗanuwansa amma ba a yi masa gwaji ba kuma ba a ba shi magani ba.

Dama dai a ranar 2 ga watan Satumbar da muke ciki ne wata Kotun Musuluncin da ke shari'ar Malamin ta umarci a yi masa gwajin kwakwalwa da kunne a wani zaman ci gaban shari'ar da aka yi.

Kotu ta bayar da umarnin ne bayan ya gaza amsa tambayoyin da alƙalin kotun Mai Shari'a Sarki Ibrahim Yola ya yi masa ranar 2 ga watan.

Wata kotu ta umarci Najeriya ta biya Sunday Igboho Naira biliyan 20

Wata kotu a jihar Oyo ta umarci gwamnatin tarayya ta biya jagoran ƴan awaren Yarabawa, Sunday Igboho Naira biliyan 20 ranar Juma'a 17 ga watan Satumba.

Babbar kotun ta ce kuɗin diyya ne bisa lalata masa gida da gwamnatin tarayya ta yi a lokacin da jami'an tsaro su ke nemansa ruwa a jallo.

Kotun ta ɗauki matakin ne bayan da Sunday Igboho ya shigar da ƙarar hukumar bincike na farin kaya da gwamnatin tarayya inda ya buƙaci su biya shi diyyar Naira biliyan 500 kan lalata masa gida a lokacin wani samame.

Ranar 1 ga watan Yulin 2021 ne jami'an tsaro suka kai samame gidan Sunday Igboho kuma suka kama mutane da dama.

Read full article