BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023
Source: BBC
Hausawa kan ce komai ya yi farko, zai yi ƙarshe!
A Larabar nan ne aka rufe majalisar wakilan Najeriya, bayan ta shafe shekara huɗu tana aiki.
An rufe majalisar ne bayan wani zaman bankwana da ta yi a ƙarshen zangonta.
Sai ranar Asabar 10 ga watan Yuni, majalisar dattijai ta tara za ta yi zama don kammala wa'adinta
Shekara huɗu ke nan, majalisar ta yi tana zartar da dokoki da ƙudurori da batutuwa da shawarwari, baya ga bibiyar ayyukan ɓangaren zartarwa.
Majalisar ta yi aiki ne a wani lokaci mafi ƙalubale tun bayan komawar Najeriya kan tsarin dimokuraɗiyya a 1999, saboda annobar korona da karayar tattalin arziƙin da ƙasar ta fuskanta har sau biyu a zamaninta.
Muhammadu Buhari da ya yi aiki tare da majalisar dokokin ta tara, ya sha yabon ta saboda haɗin kan da ya ce ta ba shi wajen amincewa da muhimman manufofi da dokokin gwamnatinsa.
Su ma 'yan majalisar wakilan a ƙarƙashin jagorancin Femi Gbajabiamila sun ce majalisa ta tara ta yi matuƙar taka rawar gani wajen kafa dokokin da za su taimaka wa ci gaban Najeriya.
Ko waɗanne muhimman dokoki majalisar ta samar a zamaninta?
1. Gyara dokar zaɓe
Masharhanta a harkokin siyasa a Najeriya na cewa nasarar babban zaɓen ƙasar na 2023 da aka samu, na da alaƙa da gagarumar gudunmawar majalisa ta tara, wadda ta yi aikin gyaran kundin dokar zaɓe.
A ranar 25 ga watan Fabrairun 2022 ne shugaban ƙasar na wancan lokaci ya sa hannu a kan kundin dokar zaɓen yayin wani takaitaccen biki wanda shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilai suka halarta.
Dokar dai ta kawo sauye-sauye kan yadda ake gudanar da zaɓe kuma ta kawo tanade-tanaden amfani da fasaha domin tabbatar da zaɓuka masu inganci da tsafta.
Wani ɗan majalisar wakilai Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya ce ta hanyar amfani da na'urar BVAS da fasahar IREC da ke tabbatar da ganin an yi zaɓuka a fayyace ba tare da nuƙu-nuƙu ba.
Haka zalika dokar ta haramta wa masu riƙe da muƙaman gwamnati jefa ƙuri'a a zaɓen shugabannin jam'iyya ko zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyu.
Su ma dai wasu 'yan fafutuka kamar Auwal Musa Rafsanjani daga CISLAC - ƙungiyar da ke ayyukan bunƙasa wayar da kai game da ayyukan majalisa ya ce gyaran dokar zaɓe da majalisa ta tara ta yi, wani muhimmin ƙoƙari ne da ya taimaka wajen ƙarfafa tsarin mulkin Najeriya da bunƙasa dimokuraɗiyya.
2. Dokar man fetur
A watan Agustan 2021 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan dokar bunƙasa harkokin man fetur (Petroleum Industry Bill) wata ɗaya bayan majalisun dokokin ƙasar sun amince da ita.
An shafe tsawon sama da shekara 20, ana taƙaddama da ce-ce-ku-ce ba tare da an zartar da dokar ba.
Auwal Rafsanjani ya ce kafa dokar zai iya kawo gyara a kan yadda ake badaƙala da cuwa-cuwa a harkokin man fetur da kuma sauran ma'adanai.
A cewarsa, "An daɗe ana fama da cin hanci da rashawa tun bayan kafa tsarin dimokuraɗiyya wajen haƙar ma'adanai kamar man fetur".
"Ƴan majalisa ta tara sun haɗa hannu kan wannan doka da ƙungiyoyin sa-kai da masu yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran 'yan kasuwa don ganin an ɓullo da dokar da za ta rage cin hanci da sace-sacen man fetur," in ji shi.
Tun a lokacin, shugaban Kamfanin Man fetur na Najeriyar NNPC, Alhaji Mele Kyari ya kare dokar da cewa tana da matuƙar muhimmanci.
"Dokar wata gagarumar nasara ce ga Najeriya da kuma sashen haƙar man fetur gaba ɗaya."
3. Dokar yaƙi da ta'addanci
A watan Oktoban 2022 ne shugaban Najeriya ya sanya hannu a kan dokar yaƙi da kuma haramta ta'addanci da aka yi wa gyaran fuska da dokar yaƙi da halasta kuɗin haram.
Sabuwar dokar yaƙi da ta'addancin ta maye gurbin wata takwararta da aka yi a shekara ta 2011, bayan garambawul ɗin da majalisa ta tara ta yi.
Wasu masana a lokacin sun ce dokar yaƙi da ta'addancin za ta samar da wani ingantacce kuma dunƙulalle sannan bakandamen tsari na doka da na bibiyar harkokin aiki da dokar wajen ganowa da riga-kafi da haramtawa da gurfanarwa gaban kotu da hukunta duk wani aikin ta'addanci.
Da kuma masu samar da kuɗaɗe don aiwatar da ta'addanci da bunƙasa ta'addanci da baza miyagun makaman hallaka ɗimbin jama'a.
Ƙwararru a Najeriya sun ce dokar za kuma ta bai wa Najeriya ikon ayyana wani mutum ko wata ƙungiya a matsayin ɗan ko 'yar ta'adda ko kuma mai samar da kuɗi ga ayyukan ta'adda. Za kuma ta bai wa kotun Najeriya ƙarin hurumi dangane da batun samar da kuɗi don kai hare-haren ta'addanci.
4. Dokar hukumar kula da almajirai
A ƙarshe-ƙarshen mulkinsa ne, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar kafa wata hukuma da za ta kula da sha'anin almajiranci da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta don kare su daga shiga halin ni-'ya-su da kuma ci da gumi.
Ɗan majalisar wakilai Balarabe Shehu Kakale da ƙarin mutum 18 ne suka ɗauki nauyin dokar mai taken: “Ƙudurin dokar kafa Hukumar Ƙasa a kan Ilmin Almajiranci da Yaran da ba sa Zuwa Makaranta don Samar da Dunƙulallen Tsarin Ilmi da nufin Daƙile Fitinar Rashin Ilmi, Ɓullo da Tsarin samar da ƙwarewa da Sana'o'i da Kare Matasa daga Fatara da Kangarewa da Shiga Halin Ni-'Ya-Su a Najeriya; da Batutuwan da suka Danganci Haka (HB.2023),”
Jim kaɗan bayan sanya hannu a kan dokar, Balarabe Kakale ya bayyana zartar da ƙudurin dokar a matsayin wata kyauta ga yaran Najeriya.
Ya ce dokar ta yi fama da matsananciyar adawa daga sassa daban-daban da kuma ƙungiyoyi a Najeriya tun bayan gabatar da ita a zauren majalisa ta tara.
Akwai miliyoyin ƙananan yara a Najeriya da ke gararamba a kan tituna ba tare da zuwa makaranta ba.
Haka zalika, masu fafutuka sun shafe tsawon shekaru suna kiraye-kirayen a ɓullo da matakan kula da tsarin karatun almajiranci a ƙasar.