You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782239

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

    

Source: BBC

Mutanen da ke rayuwa a maƙabarta mafi girma ta Kaduna

Mallam Abdulwahid Abdulsalam da Mallam Abdulaziz Ibrahim Mallam Abdulwahid Abdulsalam da Mallam Abdulaziz Ibrahim

Rukunin wasu mutane ne suka sadaukar da rayuwarsu kacokan wajen hidimtawa al'umma a maƙabarta mafi girma ta jihar Kaduna.

Tsawon gomman shekaru kenan yanzu, waɗannan mutanen su kimanin 17 suke aikin haƙa kabari da binne gawa da tsaftacewa da kuma kula da maƙabartar Tudun Wada.

A cikin wadannan jajirtattun mutane, akwai Mallam Abdulwahid Abdulsalam mai shekara 57.

Magidancin dai ya shaida wa BBC Pidgin cewa ya shafe tsawon shekara 25 yana aiki a maƙabartar har ma yana ganin ta zama tamkar gida a gare shi.

“Lokacin da muke shafewa a maƙabartar nan, ya fi wanda muke yi a haƙiƙanin gidajenmu tare da iyalanmu.

Kuma idan muna son mu ci abinci muna yin amfani da kwalayen da ake amfani da su wajen binne gawa, mu zauna mu ci abinci har ma mu kwanta mu yi barci idan akwai buƙatar haka.”

Abdulwahid ya ce yana barin gidansa tun misalin ƙarfe 7:30 na safe a kullum don fara aiki, inda yakan wuni a maƙabarta har zuwa dare kafin ya koma gida.

“Wasu lokuta, mutane sukan kira mu har cikin dare bayan mun tashi daga aiki, inda za su ce ga shi sun kawo gawa, kuma a irin wannan yanayi za mu jingine duk abin da muke yi a gida, mu zo mu taimaka a binne mamaci.”

Ya ce aikin da suke yi, ba na albashi ba ne kamar yadda gwamnati takan biya ma'aikatanta, amma duk da haka ba sa ƙasa a gwiwa saboda sun sani cewa ladansu yana wajen Allah.

“Abin da ya sa muke wannan aiki shi ne, nan ne gidan kowa na ƙarshe, kuma muna yin wannan sadaukarwa ce saboda Allah.”

“Akwai dangi da 'yan'uwana da aka binne a maƙabartar nan, kuma ni ma mai yiwuwa ne a nan za a binne ni, don haka wannan aiki tamkar yi wa kai ne.”

“Wani lokaci bayan an binne mamaci mukan cire hulunanmu mu zagaya cikin mutane ko za mu samu sadaka daga wajen waɗanda suka kawo gawa.

To da ɗan abin da muka samu ne muke zuwa mu ciyar da kanmu da kuma iyalanmu.”

Abokin aikin Abdulwahid shi ma ya yi jawabi

Abokin aikinsa mai suna Mallam Abdulaziz Ibrahim ya fara aikin haƙa kabari ne tsawon shekara 31, kuma ya ce ba zai damu ba idan wani a cikin 'ya'yansa ya bi sawunsa a wannan sana'a da ya sadaukar da rayuwarsa a kai.

“Zan yi farin ciki idan wani a cikin 'ya'yana ya zaɓi yin wannan aiki, saboda abu ne mai kyau ga lahirarsa.”

A cewar Abdulaziz a cikin maƙabartar Tudun Wada ne aka binne mahaifinsa da kawunsa, kuma a ko da yaushe yakan ziyarci kaburburansu ya yi musu addu'a.”

“A nan suka yi aiki su ma kafin rasuwarsu. A haƙiƙanin gaskiya ma mahaifina ya taho aiki nan ne, lokacin da ya gamu da tsautsayi a wajen ƙofar can, kuma wannan lamari shi ne ya zama ajalinsa.”

Masu haƙa kabarin a maƙabartar Tudun Wadan Kaduna dai sun yi kira ga gwamnati da ma ɗaiɗaikun mutane, su tallafa musu don kuwa hatta kayan aiki da suke amfani da su, sai sun aro wasu.

“Hatta shebur da diga, wasu a cikinmu sai sun karɓo aro sannan su zo aiki, to don haka muna matuƙar buƙatar tallafi da zai ba mu ƙwarin gwiwar ci gaba da wannan aiki.”

Yadda ake binne mamaci

Mallam Abdulwahid Abdulsalam ya ce da zarar an kira su cewa ga mutum ya rasu, nan take ba tare da wani ɓata lokaci ba suke fara aiki.

“Da farko dai, sai ya kasance mamacin nan Musulmi ne, saboda wannan maƙabartar Musulmai ce bayan haka za mu tambayi mutumin da ya kirawo mu, ya ba mu sanarwar cewa an yi mutuwa, mu ji shin mamacin nan mai ƙiba ne ko kuwa siriri ne.”

“Abin da ya sa muke tambayar girman jikin mamaci shi ne don a auna masa kabari daidai wa daida saboda yanayin girman jikin gawa, haka yanayin girma da tsayin kabarinta.”

“Aikina shi ne na tabbatar an yi komai gwargwadon yadda aka tsara saboda idan an kawo gawa, ni ne zan sanya ta a kabari,” in ji shi.

‘Na haƙa kaburbura fiye da 70,000’

Mallam Abdulaziz Ibrahim ya ce ya haƙa kaburbura fiye da 70,000 da aka binne gawawwaki a tsawon shekarun da ya kwashe yana aiki a maƙabartar Tudun Wada.

“Wasu lokutan a rana ɗaya muna iya haƙa kaburbura kamar 20, wasu ranakun kuwa mu haƙa kaburbura ƙalilan, ya danganta kawai da adadin mutanen da suka mutu a rana.”

‘Ana yaudarar mutane da zancen fatalwa a fina-finai’

Abdulaziz ya ci gaba da cewa yadda ake nuna fatalwa a fina-finai, duk ba gaskiya ba ne, a cewarsa duk lokacin da ya ga irin waɗannan surori a fim sai ya yi ta dariya.

“A fim wasu lokuta sai ka ga an nuna wai fatalwa ko fatalyi sun biyo mutum da gudu, duk wannan shiri ne saboda a rayuwa ta zahiri babu wani abu mai kama da haka.”

“Tun da na fara aiki ranar 2 ga watan Yulin 1992 ban taɓa ganin wanda ya ce ya ga fatalwa ba, kuma ni ban taɓa ganin abin da ya tsorata ni a nan ba.”

‘Ranar da ba zan taɓa mantawa ba’

A cewar Abdulwahid ranar da ba zai taɓa mantawa da ita ba a wannan aiki nasa ita ce sa'ar da aka yi wani hatsari da ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 18 a lokacin da suke tafiya inda aka kawo gawawwakin maƙabartar Tudun Wada don a binne.

“Wannan ranar ce ba zan taɓa mantawa da ita ba a tsawon shekarun aikina, dalilin hatsari duk waɗannan mutane suka mutu don haka, rana ce mai cike da matsanancin juyayi da baƙin ciki saboda ga ƙananan yara nan da mata sun biyo su, an taho.

Mallam Abdulwahid da abokin aikinsa Abdulaziz dai sun ce za su so a ce 'ya'ya da danginsu sun kawo su maƙabartar Tudun Wada a binne su idan ta-Allah ta kasance a kansu, kamar yadda aka binne wasu makusantansu a ciki.

Read full article