BBC Hausa of Sunday, 21 May 2023
Source: BBC
Mutum 12 ne suka mutu a turmitsin kallon tamaula a San Salvador a kasar El Salvador, kamar yadda mahukunta suka sanar.
Lamarin ya faru a lokacin wasan hamayya tsakanin Alianza da Santa Ana, wadanda ke buga wasa filin da ake kira Fas at Cuscatlán.
Kawo yanzu an dakatar da wasan nan take.
Tun farko 'yan sanda sun sanar cewar maza bakwai da mata biyu suna cikin wadanda suka rasa rai, wadanda suka haura shekara 18 da haihuwa.
Lamarin ya faru ne, bayan da wasu sashen 'yan kallo makil suka yi kokarin shiga sitadiya da karfin tuwo, bayan da aka garkame kofofin shiga.
Mahukunta sun ce magoya baya sun sayar da jabun tikitin kallon wasan, wanda a lokacin ana tsaka da bincike.
Wasu bidiyoyi da aka nuna anga magoya baya na kokarin karya wani shinge na harabar da zai baka damar shiga ginin filin wasan.
Hukumar kwallon kafar ta El Salvador ta soke dukkan karawar ranar Lahadi.