You are here: HomeAfricaBBC2022 10 02Article 1634594

BBC Hausa of Sunday, 2 October 2022

    

Source: BBC

Mutum 174 sun mutu a filin tamaula a turmutsitsi a Indonesia

Hoton zanga zanga da aka yi a filin wasa Hoton zanga zanga da aka yi a filin wasa

Aƙalla mutum 174 ne suka rasu sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a yayin da ake buga wasan ƙwallon ƙafa.

Rahotanni sun ce aƙalla mutum 180 ne suka samu raunuka a yayin turmutsutsun.

Rahotanni sun ce mummunan lamarin ya faru ne bayan ƙungiyar Arema FC ta yi rashin nasara a wasan da aka buga a filin wasan da ya cika maƙil da mutane a Malang a ranar Asabar da dare.

Turmutsutsun ya faru ne bayan da ƴan sanda suka harba hayaƙi mai sa hawaye ga ƴan kallon da suka kutsa cikin filin wasan.

Sakamakon hankalin jama'a da ya tashi bayan harba hayaƙi ma isa hawayen, sai mutane kowa ya nufi hanyar fita filin wasan inda a wannan dalili ne jama'a da dama suka suƙe, wasu kuma aka tattake su.

Tun da farko dai rahotanni sun ce mutum 130 ne suka rasu, amma daga baya hukumomi a ƙasar sun sanar da cewa adadin ya ƙaru zuwa 174 inda kuma akwai mutum 11 da suka ji mummunan rauni.

Tuni dai Shugaba Joko Widodo na ƙasar ya bayar da umarni kan cewa a dakatar da duk wasu manyan wasanni na gasar ƙwallon ƙafa ta Indonesia har sai an gudanar da bincike.

Read full article